'Mun shiga tashin hankali lokacin da kyauren jirgi ya fadi'

Fasinjoji sun ce jirgin ya yi ta jijjiga Hakkin mallakar hoto A picture of the inside of the aircraft posted on
Image caption Fasinjoji sun ce jirgin ya yi ta jijjiga

Wani fasinja da ke cikin jirgin sama na kamfanin Dana a Najeriya, ya ce ba karamin tashin hankali ya shiga ba a lokacin da kyauren jirgin saman ya fadi suna ciki.

Kyauren jirgin saman ya fadi ne a lokacin da ya sauka yake kuma kokarin tsayawa a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, babban birnin kasar.

Sai dai kamfanin jiragen sama na Dana ya dora laifin hakan a kan wani fasinja, da cewa ya yi kokarin bude kyauren ne shi ya sa kyauren ya fado.

Batun faduwar kyauren dai ya mamaye kafofin watsa labarai da shafukan sada zumunta na kasar.

Fasinjan mai suna Dapo Sanwo, ya shaida wa BBC cewa:

"Kara ta cika jirgin kuma ya yi ta girgiza. Sai na lura cewa daya daga cikin kyaurayen jirgin ya zazzago yana rawa.

A lokacin da muka sauka jirgin ya fara kokarin tsayawa a wajen tsayuwa, sai muka ji wata kara kamar fashewar bam, sai kuma muka ji iska kadawa sosai da kuma hayaniya.

Abun babban tashin hankali.

Ma'aikatan jirgin sun yi kokarin cewa wani fasinja ne ya jawo marfin kyauren, amma sai kowa duk wadanda suke cikin jirgin suka musanta hakan.

"Sun kuma yi kokarin hana mu daukar hotuna da bidiyo."

Kamfanin jirage na Dana ya ce abu ne mai matukar wahala a ce kyauren jirgin sama ya fadi da kansa "in dai ba wani fasinja ne ya yi kokarin bude shi ba.'

Tun a ranar Laraba da abun ya faru masu amfani da shafin sada zumunta na Twitter suka fara yada batun cewa rashin kula da al'amura ne daga kamfanin ya sa hakan faruwa.