Rwanda: Mata ba za su samu rahamar Ubangiji ba - Fasto

Rights groups are horrified after a preacher said there was nothing good about women Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan al'amari ya harzuka kungiyoyin 'yancin dan adam

Hukumar da ke sa ido kan kafofin watsa labarai a Rwanda za ta yi wa wani fasto sammaci bayan da ya ce mata ne silar duk wani bala'i, yayin da yake wa'azi a wani gidan rediyo.

Fasto Nicolas Niyibikora ya shaida wa masu sauraro cewa: "mata ba sa tare da rahamar Ubangiji" yayin da yake wa'azi a gidan rediyon Amazing Grace a watan Janairu, yana gargadin cewa "babu wani abu mai kyau da ke tattare da mata."

Ya tambayi masu sauraronsa: "Idan kun karanta baibul, waye ya fara yin zunubi a duniya? Sai ya ce: "Ai ba namiji ba ne."

Wannan al'amari ya harzuka kungiyoyin 'yancin dan adam, inda har suka yi taron manema labarai, suna gargadin cewa irin wadannan kalaman "za su iya jawo kiyayya da rikici a tsakanin 'yan Rwanda idan har ba a yi wani abu da gaggawa a kai ba", a cewar Jaridar Rwandan Times.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun kai korafi hukumar da ke sa ido kan kafofin watsa labarai ta kasar RMC, wadda za ta shirya taro don tattauna batun a mako mai zuwa.

Emmanuel Mugisha ya shaida wa New Times cewa ko gidan rediyon ma sai ya zo ya yi bayani kan lamarin.

Dama dai mabiyan Mista Niyibikora, sun dan dinga ja baya da shi, saboda an taba korarsa daga kasar shekara biyar da suka gabata.

Labarai masu alaka