Yadda sojojin Cameroon suka min tsirara — 'Yar gudun hijira

  • Ishaq Khalid
  • BBC Hausa
'Yan gudun hijirar Cameroon

Jami'an hukumar agaji a Najeriya sun bayyana cewa 'yan gudun hijira fiye da 40,000 ne suka shiga kasar daga kasar Kamaru mai makwabtaka a kwanakin baya.

Yayin da suka ce adadin na karuwa a kullum, Hukumar Kula da 'yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mata da kananan yara cikin 'yan gudun hijirar sun fi fuskantar hadari.

'Yan gudun hijirar suna dai gudu ne daga kudancin Kamaru, inda sojojin kasar ke dirar mikiya kan 'yan-aware masu neman kafa kasar da suke kira Ambazonia a yanki mai magana da harshen Ingilishi, saboda abin da suka kira "mulkin wariya na 'yan yankin renon Faransa".

Suna zargin 'yan yankuna masu magana da Farasancin da takura masu ta fuskar damar samun ayyukan yi, da ilimi da kiwon lafiya da kuma harkokin siyasa da shugabanci.

Galibin 'yan gudun hijirar na zaune ne a garuruwa da kauyuka na kan iyaka a jihar Cross River da ke kudancin Nijeriya, kodayake akwai wasunsu a jihohi kamar Benue da ke arewa ta tsakiyar kasar.

Suna dai bayyana irin mawuyacin hali da suka shiga.

'Kwana takwas ina tafiya a kasa cikin daji'

Dubban iyalai ne dai aka raba da gidajensu a yankin na kudancin Kamaru renon Birtaniya.

Mista Rene da matarsa da 'ya'yansa sun tarwatse sakamakon samamen sojojin Kamaru a kauyensu inda sojojin suka yi kaca-kaca da kauyen suka kuma kashe mutane da dama, kamar yadda ya bayyana wa BBC.

Matarsa da 'ya'yan nasa sun yi sa'a wadansu mutane sun rage masu hanya da babur bayan da suka yi tafiya ta tsawon sa'o'i da dama a kasa.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

To amma shi ya kwashe fiye da mako guda yana dabar sayyada, ma'ana yana tafiya a kasa, domin tserewa.

Ya ce tsawon lokacin baya cin abinci illa 'ya'yan ice da amfanin gonar mutane idan ya tarar a hanya.

Ya yi debuwa kusan kwana biyu a daji kafin daga bisani ya hau wata hanyar kafa wadda ta bulla da shi wani kauye da ake kira Bashu a jihar Cross River da ke Najeriya, inda ya yi dace, ya gamu da iyalinsa cikin wasu 'yan gudun hijirar.

Rene ya ce: ''Muna zaune lami lafiya a kauyenmu, kwatsam sai sojojin gwamnatin Kamaru suka kutsa wa al'umarmu, cikin mintuna kadan sai muka fara jin karar harbe-harben bindiga, mu kuma muka fara guje-guje, ba mu ma san inda muka dosa ba."

"Wasunmu mun kwashe kwana takwas a cikin daji. Har yanzu akwai wasu dangina da ban san inda suke ba,'' in ji shi.

Yanzu dai Rene mai shekara 32, tare da iyalinsa, na zaune a garin Ikom da ke jihar Cross, kimanin Kilomita 27 daga kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Ya nuna mani irin munanan raunuka da ya samu a kafarsa sanadiyyar kwanaki da dama da ya shafe yana tafiya cikin daji.

Kodayake yana da kyakkyawan fatan wata rana yankin Kamaru mai magana da Ingilishi zai samu mulkin kai, to amma ya ce ba zai koma kasar Kamaru ba, sai ya tabbatar da zaman lafiya ya samu a yankin nasu.

'Sojoji sun yi wa mata zindir'

Da dama daga cikin 'yan gudun hijirar na Kamaru na batun cewa jami'an tsaron kasar sun yi masu abubuwan cin zarafi. Mata da dama sun ce sojoji sun yi masu zindir tare da wulakanta su.

Nguma, mai shekaru kasa da 30, ta yi zargin cewa sojojin jamhuriyyar Kamaru sun yi wa ita da wadansu mata ayyukan na keta haddi.

Bayanan hoto,

Nguma ta ce sojin Kamaru sun keta musu haddi

Ta ce ''sun yi mana duka, suka tube mu zindir, kana suka jefa mu cikin rafi.''

Daga bisani dai wasu 'yan gudun hijirar da ke tafiya a kwale-kwale sun taimaka masu suka kwashe zuwa cikin Najeriya.

Nguma ta ce ko da yake ita ba a yi mata fyade ba, to amma tana da labarin sojoji sun yi wa wadansu matan fyade.

Wata matar mai suna Regina, ta shaida wa BBC cewa wasu sojojin uku sun sa ta a gaba, yayin da take sauri domin debo 'ya'yanta a gida lokacin da tarzoma ta barke a kauyensu.

Ta yi zargin cewa daya daga cikin sojojin ya cukume ta yayin da suka isa gidan nata.

''Idan mutum ba mijinka ba ne, kuma ya damke maka kirji, ya cukume ka, ai sai ka tsorata. Don haka na tsorata kwarai, domin an ce sojoji suna yi wa mutane fyade."

Ta ci gaba da cewa "daga nan na fara ihu. Da sojojin suka ga yarana na fitowa sai suka kyale ni, suka tafi.''

Gwamnatin Kamaru wacce 'yan yankin renon Faransa suka fi rinjaye a cikinta, ta musanta zargin cin zarafin jama'a a yankin na renon Birtaniya.

Kakakin gwamnati Issa Tchiroma Bakary, ya shaida wa BBC cewa sojojin na kokarin kare martabatar kasar ne kurum da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin na kudancin Kamaru inda 'yan-aware ke yunkurin kafa kasar da suka kira Ambazonia.

Ya ce Kamaru ba za ta lamunci wani yankinta ya balle ba.

To amma ya ce a shirye gwamnatin take ta tattauna da masu korafi.

Duk da musanta zarge-zargen cin zarafi da keta hakkin bil-Adama da hukumomi ke yi, da dama daga cikin 'yan gudun hijirar da suka tsallako zuwa Najeriya na cewa har yanzu a kidime suke sanadiyyar tashin hankali da suka gani samakon samamen sojojin na Kamaru.

Misis Regina ta ce ''Idan muka samu milki kanmu zan koma. To amma idan yakin bai kare ba, ba zan koma ba domin ina jin tsoron sojoji. Duk lokacin da na ji karar manyan bindigoginsu, ko na tuna, sai in ji kamar zan mutu. Ba zan iya rayuwa da irin wadannan bindigogi a cikin Kamaru ba.''

'Yan gudun hijirar dai na cikin rashin tabbas game da makomarsu a Kamaru inda suka tsere, da kuma makomarsu a Najeri ya inda suke samun mafaka.

'Mutum guda ya dauki nauyin 'yan hijira 28'

Galibin 'yan gudun hijirar fiye da dubu arba'in wadanda suka shigo ta hanyoyi masu wahala, yanzu suna zaune ne a gidajen daidaikun mutane talakawa domin babu sansanoni na hukuma.

'Yan kasar Kamarun na cewa suna fama da karancin abinci, da rashin muhimman kayakin kiwon lafaiya, yayin da yara basa iya zuwa makaranta.

Galibin yaran sun zo ne ba tare da iyayensu ko kuma wani danginsu babba ba, lamarin da ya kara raunana su, a cewar hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinki Duniya.

Hukumomin agaji na cewa a wasu wuraren, adadin 'yan gudun hijirar ya ninka adadin mazauna kauyukan da suka sauka.

To sai dai kuma, wasu daga cikin mazauna kauyuka da garuruwan na daukar nauyin 'yan gudun hijirar, duk da cewa su ma matalauta ne.

Mista Frank Okoro, wani malamin makaranta mai mata daya da 'ya'ya hudu, ya bai wa 'yan gudun hijirar Kamaru 28 masauki, yana kuma kula da su a kauyen Abokim. Mutumin mai shekaru 57, ya ce:

Bayanan hoto,

Mista Okoro ya ce ya dauki nauyin mutanen ne saboda irin mawuyacin hali da ya gansu a ciki

''Ina tare da iyalai takwas a nan; wato baki dayansu, ina da mutane 28 tare da ni. Cikin rahamar Ubangiji, ka san daga waje sai ka ga gida dan kankane, amma a ciki, musamman da dare, sai ka ga kowa ya samu wurin kwana, kuma da safe a farka a matsayin abu guda. Mukan shimfida masu tabarmi. Kusan dukkan yaran kan kwanta a kasa, ko a kan tabarmi ko kuma a kan zannuwan iyayensu mata. Matsawar dai za su yi barci su tashi lafiya da safiya bukata ta biya''.

Mista Okoro ya ce ya dauki nauyin mutanen ne saboda irin mawuyacin hali da ya gansu a ciki, da kuma irin kyakkyawan tasiri da zumunta da ke tsakanin al'umomin jihar Cross River da na yankin tsallaken iyaka na cikin Kamaru.

Ya ce yana iya kula da dimbin mutanen ne tare da taimakon Allah. Ya kara da cewa su ma wadansu daga cikin suna da kwazo, don haka idan suka ga yana aiki, alal misali na gona, sukan taimaka.

Kalubalen dake gaban hukumomin Najeriya

Dama dai Najeriya na fadi tashin yadda za ta kula da mutane fiye da miliyan biyu da ricikin Boko Haram ya raba da muhallansu a arewacin kasa - don haka dawowar 'yan gudun hijirar rikicin Kamaru zuwa Najeriya ta kasance wani karin kalubale.

Galibin 'yan gudun hijirar Kamarun na zaune a jihohin Cross River da ke kudancin Najeriya da Binuwai da ke arewa ta tsakiyar kasar.

Hukumomin Najeriya na cewa aikin da na wahalar gaske amma dai suna bakin kokarinsu, kamar yadda Mista John Inaku, shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar Crsoss River ya bayyana.

Bayanan hoto,

'Aikin na da wahalar gaske'

''To kawo yanzu aikin na da wahalar gaske, kuma abin takaici ne ka ga mutane na ta tudadowa, musamman idan baka yi masu tadadi ba. Yana da wahala ka kimtsa su wuri guda. Don Haka abin da muka yi a lokacin da muka fara ganin alamar haka, sai muka dukufa aiki domin ganin yadda za mu wayar da kan jama'ar kauyuka da garuruwa na kan iyaka da Kamaru.''

Sauran wadanda ke kokarin kula da 'yan gudun hijiar Kamarun sun hada da Hukumar Kula da 'yan Gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR, da kungiyar agaji ta Red Cross da dai sauransu.

Tuni dai hukumar UNHCR ta gargadi Najeriya game da mayar da 'yan kasar Kamaru masu neman mafaka a hukumance a Najeriya kasarsu ta asali, tana mai cewa kamata ya yi Najeriya ta rika kiyayewa da dokokin kasa da kasa wadanda suka jibinci 'yan gudun hijira.

Hukumomin ba da agaji na cewa adadin 'yan gudun hijirar Kamarun ka iya wuce miliyan daya nan da 'yan watanni muddin ba a samu zaman lafiya a inda suke fitowa ba.

Dangantakar Najeriya da Kamaru kan batun a-ware

Najeriya da Kamaru dai kasashe ne makwabtan juna wadanda suka dade suna hulda tare ko da ya ke daga lokaci zuwa lokaci sukan samu tsamin dangantaka.

Alal misali, kasashen biyu sun yi takaddama mai zafin gaske kan batun mallakar yankin nan mai dimbin arzikin man fetur na Bakassi kafin daga bisani Najeriya ta mika wa Kamaru yankin sakamakon wani hukuncin kotun kasa da kasa a 2002, da kuma sanya hannu kan wata yarjejeniya da ta samu goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.

To amma kasashen a halin yanzu suna da muradu masu kama da juna kan batun masu fafutikar ballewa daga kasashensu.

Ko a kwanakin baya, hukumomin Najeriya sun kama wasu daga cikin masu fafutikar ballewa daga yankin Kamaru mai magana da harshen Ingilishi domin kafa kasar Ambazonia.

Rahotanni sun ce an kama su ne a Abuja yayin da suke taro, kana daga bisani hukumomin Kamaru suka bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta mika mata su kuma za su fuskanci shari'a, kamar yadda Kakakin gwamnatin Kamarun, Issa Tchiroma Bakary, ya shaida wa BBC.

Haka nan jami'an gwamnatocin kasashen biyu sun bayyana cewa akwai hadin kai matuka a tsakaninsu da nufin dakile batun a-ware.

Wannan batu na hadin kai ba abin mamaki ba ne, a cewar masu lura da lamaru.

Najeriya da Kamaru na bukatar taimakon junansu domin suna da matsaloli iri guda.

Najeriya na fuskar matsalar masu kokarin ballewa domin kafa kasar Biafra a kudu maso gabashin kasar, kuma kasar Kamaru ita ce kasar da ta fi kusa da wannan yanki, idan ana batun makwabtaka ta fuskar iyaka.

Haka nan ta fuskar iyakar kasa, Najeriya ita ce kasar da ta fi kusa da yankin Kamaru mai magana da harshen Ingilishi, yankin da ke kokarin ballewa daga kasar Kamaru.

Don haka, masu lura da lamura na cewa kalubalen iri guda ne.

Haka zalika, wani babban kalubale da kasashen biyu ke fuskanta shi ne na kungiyar Boko Haram, wadda tuni ta yi masu mummunar barna.

Sojojin kasashen biyu na yaki tare domin ganin bayan wannan kungiya wadda ta fi karfi a arewacin Najeriya.

Bisa dukkan alamu, kasashen na Najeriya da Kamaru na taka-tsan-tsan wajen tunkarar lamuran na 'yan-aware domin kada bango ya tsage.

To amma a halin da ake ciki, abin da babu tabbas shi ne tsawon lokaci da wannan hadin kai zai ci gaba da wanzuwa, da tsawon lokacin da 'yan gudun hijirar Kamaru za su kasance a Najeriya, da ma tsawon lokacin da za a dauka kafin a kai ga warware batun na ballewa da jama'ar yankin Kamaru renon Birtaniya ke yi.