Wani jami'in gwamnatin Nigeria ya 'mallaki motoci 86'

Ana tuhumar jami'in gwamnatin Najeriya da mallakar motocin alfarma 86
Bayanan hoto,

Ana tuhumar jami'in gwamnatin Najeriya da mallakar motocin alfarma 86

Wata babbar kotu a Najeriya na tuhumar wani babban jami'in gwamnatin kasar Ibrahim Tumsah da kaninsa Tijjani, da kin tabbatar da wanda ya mallaki motocin alfarma 86 a cikinsu.

Ibrahim Tumsah, shi ne babban darakta mai kula da harkokin kudi a ma'aikatar makamashi, ayyuka da kuma gidaje ta kasar.

Mutanen biyu, ana kuma zarginsu da kin bayyana kadarorinsu ba tare da kwararan dalilai ba.

Sai dai a baya mutanen sun sha musanta irin wannan zargin.

Wani kwamiti na musamman da shugaban Najeriyar ya kafa don gudanar da bincike da kuma bankado kudaden gwamnati da aka sace ne ya bukaci Ibrahim Tumsah da kaninsa a kan su bayyana ko motocin waye.

Yanzu haka dai an bayar da belinsu a kan kudi naira miliyan 20, tare da umartarsu a kan su sake bayyana gaban kotu domin ci gaba da shari'ar da ake musu a cikin wata mai kamawa.