Nigeria: An kama lauyan bogi a Lagos

idris kpotun

Asalin hoton, Nigeria Police

Rundunar 'yan sandan jihar Lagos da ke kudancin Najeriya ta kama wani mutum da laifin zama lauyan bogi a jihar.

An kama mutumin ne bayan gano cewa lauyan karya ne a yayin da ake gabatar da wata shari'a a kotu a ranar Laraba, inda yake neman a bai wa wanda yake karewa a shari'ar beli.

'Yan sanda sun ce -- mutumin mai shekara 49 ya shafe shekara 15 yana aiki a matsayin lauyan bogi.

An fara dasa ayar tambaya a kan mutumin ne bayan da ya yi kokarin karanto wani sashe na kundin tsarin mulki don ya karfafa hujjojinsa, amma sai ya kasa yin bayanin da ya dace.

A take sai wani lauyan daban ya kalubalance hujjojin nasa.

A yanzu dai mutumin yana hannun 'yan sanda inda ake tuhumarsa.

A Najeriya dai an sha samun mutane na boge a wasu bangarorin aiki da ke bukatar kwarewa kamar aikin likita.

Ko a watan Yunin 2016 'yan sanda sun kama wani likitan bogi a Abuja babban birnin kasar, wanda ake zargi da tafiyar da wani asibiti na tsawon shekara 10 ba bisa ka'ida ba.