Komai ya tsaya cak a gwamnatin Amurka kan kasafin kudi

Sen. Rand Paul (C) (R-KY) takes a brief break from the floor of the U.S. Senate to pose for a photo with Rep. Justin Amash (L) (R-MI) and Rep. Thomas Massie (R) (R-KY) at the U.S. Capitol February 8, 2018 in Washington, DC.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Senator Rand Paul (C) poses with friends from the House during a break in proceedings

Gwamnatin Amurka ta tsayar da tafiyar da dukkan al'amura a hukumance a karo na biyu a wannan shekarar, saboda 'yan majalisa sun gaza cimma samun matsaya a kan kasafin kudi kafin ranar da aka sanya musu.

Sanatoci sun fuskanci adawa daga dan jam'iyyar republican Rand Paul, amma a yanzu sun amince da kudurin ya zama doka, inda har an aika shi majalisar wakilai don amincewa da shi.

Kudin da gwamnatin tarayya take bayarwa don gabatar da ayyukan gwamnati zai kare ne da tsakar dare daidai da karfe 5 na safe agogon GMT.

Kudurin kasafin kudin mai shafi 600 ya bukaci a kara yawan kudaden da ake kashewa da kusan dala biliyan 300, a bangaren tsaro da harkokin cikin gida.

Idan majalisar wakilai ta amince da kudurin kuma shugaban kasa ya sanya hannu nan da sa'o'i kadan, za a ci gaba da gudanar da al'amuran gwamnati da wayewar garin Juma'a a Amurka.

Amma ba a da tabbas kan yadda majalisar wakilai za ta amince da kudurin, da kuma yadda hakan zai shafi ayyukan gwamnati a ranar Juma'a idan har aka ci gaba da tsayar da al'amura.

Me tsayar da al'amuran gwamnati ke nufi gun al'ummar kasa?

Hukumomin gwamnati da dama sun kasance a rufe saboda ba su da tabbas na samun kudaden da za su ci gaba da kashewa.

An umarci ma'aikatan gwamnati kada su je aiki kuma ba za a biya su ba - duk da cewa dai za a biya wasu daga baya.

Sai dai an umarci ma'aikata masu matukar muhimmanci kamar jami'an soji da masu lura da sufurin jirgin sama su ci gaba da ayyukansu duk kuwa da tsayawar al'amuran.

Makonni uku da suka bata, wasu mutanen sun yi asarar kwanaki uku na aiki sakamakon irin wannan lamari, amma a wannan karon ba a da tabbacin hukumomin da ba za su yi aiki ba.