Su waye 'yan Afirka da za su je gasar Olymic ta hunturu?

Asalin hoton, Getty Images
An fara gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu a Koriya ta Kudu
Kasashen Afirka takwas ne za su fafata a gasar Olympics ta Hunturu na 2018 a Pyeongchang, Koriya ta Kudu, wanda za a fara ranar Jumma'a 9 ga Fabrairu.
Afirka nahiya ce mafi zafi a duniya, saboda haka ba ta da yanayin sanyi da ake bukata domin wasanni kamar tseren dusar kankara, da wasannin Bobsleigh da na snowboarding.
Amma duk da wannan matsalar, 'yan wasa daga kasashen Afirka da dama (Najeriya, da Eritriya, da Ghana, da Kenya, da Madagaska, da Afirka ta Kudu, da Maroko da kuma Togo) za su sami wakilci a gasar ta Pyeongchang 2018.
Wannan tarihi ne ake gabatarwa ga kasashe kamar Najeriya da Eritriya, wadanda a karon farko suke halartar wannan gasar Olympics ta Hunturu.
Ga cikakken bayanai game da dukkan 'yan Afirkan da za su fafata a in Pyeongchang:
-
Akwasi Frimpong
- Shekaru: 31
- Kasa: Ghana
- Wasa: Skeleton
Akwasi Frimpong ne ya kafa Hukumar Wasan Bobsleigh da Skeleton ta kasar Ghana (BSF-Ghana) a 2016.
Da farko Frimpong dan wasan gudu ne, amma wani ciwon agara ya sa shi sauya wasa.
Ya kan dauki kimanin shekara hudu zuwa shida kafin mutum ya kware akan wasan, saboda matukar gudun da ake yi a cikinsa.” -
Sabrina Simader
- Shekaru: 19
- Kasa: Kenya
- Wasa: Tseren kankara daga saman dutse
Simader ce ‘yar Kenya ta farko daga Kenya da za ta wakilci kasar a gasar Olympics na Hunturu. Iyayenta sun koma kasar Ostriya a lokacin tana da shekara uku.
Ta zama ‘yar wasan tseren dusar kankara a 2013. A 2016 ta wakilci kasarta a gasar Olympics na Hunturu matasa a birnin Norway.
Dadin da nake ji idan ina kan sandunan tseren, ina matukar gudu, sai ka ji kamar za ka zautu. Yadda jininka ke bugawa, sai kaji wani irin dadi da ‘yanci. Lokacinka ne.” -
Mialitiana Clerc
- Shekaru: 16
- Kasa: Madagaska
- Wasa: Tseren kankara daga saman dutse
Mialitiana Clerc ta fara koyon wasan tseren kankara a lokacin ta na mai shekara uku a Faransa. A ranar 16 ga watan Nuwamba 2017 ta cika shekara 16 da haihuwa, inda ta zama daya daga cikin ‘yan wasa mafi kankantar shekaru a wannan gasar ta bana.
-
Samir Azzimani
- Shekaru: 40
- Kasa: Moroko
- Wasa: Tseren dusar kankara na hawa duwatsu
Da farko Samir Azzimani ya gwada tseren sudadowa daga saman dutse ne, amma ya sauya zuwa tseren hawa duwatsu akan dusar kankara.
-
Adam Lamhamedi
- Shekaru: 22
- Kasa: Moroko
- Wasa: Tseren kankara daga saman dutse
Adam Lamhamedi, wanda ke rike da fasfunan Moroko da Kanada, ya kafa tairihi a lokacin da ya zama dan Afirka na farko da ya lashe lambar zinare a gasar Olympics na Matasa da aka yi a Ostriya a 2012.
-
Moriam Seun Adigun
- Shekaru: 31
- Kasa: Najeriya
- Wasa: Bobsleigh
Seun Adigun ce wadda ta kafa kungiyar wasan Bobsleigh ta farko a Najeriya. Ita ce mai tuki a kungiyar.
A da ita ‘yar tseren mita 100 ce kuma ta taba wakiltar Najeriya a gasar Olympics da aka yi a birnin Landan a 2012.
Abin mamaki ne… Najeriya ba ta taba samun wakilci a gasar Olympics na Hunturu ba, kuma ‘yan kasar na murnar ganin haka ya kasance. -
Akuoma Omeoga
- Shekaru: 25
- Kasa: Najeriya
- Wasa: Bobsleigh
Akuoma ita ce “mai taka birki” a kungiyar wasan Bobsleigh ta farko da aka taba kafawa a Najeriya.
Kana tana aiki a fagen daukar ma’aikatan lafiya.
-
Ngozi Onwumere
- Shekaru: 26
- Kasa: Najeriya
- Wasa: Bobsleigh
Ngozi Onwumere ‘yar wasan tsere da tsalle-tsalle ce wadda a baya ta wakilci Najeriya a gasar wasanni na dukkan nahiyar Afirka a 2015.
-
Simidele Adeagbo
- Shekaru: 36
- Kasa: Najeriya
- Wasa: Skeleton
Bayan ta bar wasanni na tsawon shekaru tara, amma Simidele Adeagbo ta sami karfin gwuiwar komawa da ta ga kungiyar Bobsleigh ta Najeriya, saboda haka ta yanke shawarar yin wasan Skeleton.
Adeagbo ce ‘yar Najeriya ta farko da za ta wakilci kasar a wannan wasan a gasar Olympics na Hunturu.
-
Connor Wilson
- Shekaru: 21
- Kasa: Afirka ta Kudu
- Wasa: Tseren kankara daga saman dutse
Connor Wilson ya yi karatun zama likitan dabbobi ne a jami’ar Vermont da ke Amurka.
-
Mathilde-Amivi Petitjean
- Shekaru: 23
- Kasa: Togo
- Wasa: Tseren dusar kankara na hawa duwatsu
A da Mathilde-Amivi Petitjean ‘yar kungiyar ‘yan tseren dusar kankara mai nisa na Faransa, amma ya sauya domin ya wakilci kasar Togo, kasar da aka haifeta.
-
Alessia Afi Dipol
- Shekaru: 22
- Kasa: Togo
- Wasa: Tseren kankara daga saman dutse
Duk da cewa Alessia Afi ba ta da ‘yan uwa a Togo domin ita haifaffiyar kasar Italiya ce, amma ta zabi ta wakilci kasar da ke yankin Afirka ta yamma.
Kuma ‘yar wasan tseren dusar kankara na dogon zango ce, kuma ta taba wakiltar Togon a gasar Olympics na Hunturu a Sochi, kasar Rasha a 2014.
-
Shannon-Ogbani Abeda
- Shekaru: 21
- Kasa: Eritrea
- Wasa: Tseren kankara daga saman dutse
A kasar Kanada Abeda ya girma, kuma ya so ya yi wasan kwallon gora na kankara, amma sai yayyensa suka ba shi shawara da ya koma tseren dusar kankara.
Shi ne dan Eritriya na farko da zai wakilci kasarsa a gasar Olympics ta Hunturu.
Na san ba kasafai ake samun dan Eritriya kamar ni ba, wanda ke wasan tseren kankara wato skiing, amma ‘yan Eritriya na da kishin kasa sosai. Idan suka ga wani na wata gasa ko wakiltar Eritriya, sai kaga suna ta murna
Photo Credits:
Matthias Hangst/Getty Images, Dimitar Dilkoff/AFP/Getty Images, Francois Xavier Marit/AFP/Getty Images, Shaun Botterill/Getty Images, Christophe Pallot/Agence Zoom/Getty Images, Alexander Hassenstein/Getty Images, ALEXANDER KLEIN/AFP/Getty Images, Dean Mouhtaropoulos/Getty Images, Courtney Hoffos