Nigeria ta kama 'yan China da zargin hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba

hakar ma'adinai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gwamnati na son inganta yanayin da leburori ke ciki, wadanda kamfanonin da ke hakar ma'adinai ke ci da guminsu

An kama wasu 'yan kasar China hudu a Nijeriya da ake zarginsu da gudanar da ayyukan hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba.

Wata rundunar hadin gwiwa ta 'yan sanda da sojoji da kuma 'yan sandan ciki, ta kama 'yan kasar Chinar, da wasu mutane 16 'yan Najeriya da ake zargin suna aiki tare da su a jihar Ebonyi da ke kudu maso gabashin kasar.

Hukumomin Najeriya dai sun sha kukan cewa hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba na janyo hasarar dimbin kudade ga tattalin arzikin kasar wanda ke tangal-tangal.

Hukumomi a jihar ta Ebonyin sun ce an kama mutanen 20 ne a wani wurin hakar ma'adanai ake Chara-Uhunu a karamar hukumar Abakaliki.

Babban Sakataren watsa labarai na gwamnan jihar ta Ebonyi, Mista Emmanuel Uzor, ya shida wa BBC cewa wannan matakin ya biyo bayan kaddamar da wani shiri ne na yaki da hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a jihar.

''Ayyukan wadannan 'yan kasar China na da matukar hadari ga lafiyar jama'a da kuma muhalli da dai sauransu, domin abin da suke yi shi ne suna tona rami, ya yi loto, su shiga karkashin kasar suna hakar ma'adanai.

Ba wai suna yi ba bisa ka'ida ba ne kawai, a a', hakar ma'adanai ne ta karkashin kasa wadda ke da hadari.

Mutum 20 din da aka kama yanzu haka suna hannun 'yan sanda ana bincike.

Suna hakar dalma ne, da ma'adanin Zinc da sauran albarkatun kasa.''

Gwamnatin ta ce akwai yiwuwar a gurfanar da mutanen da ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.

A ranar Laraba ne dai jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda da kuma 'yan sandan ciki suka kama mutanen bayan da aka tsegunta masu ayyukan, ana kuma ci gaba da tsare su.

A Najeriya dai an sha bayar da labarin kama wadanda ake zargin masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba ne da suka hada da 'yan kasashen waje, to amma ba kasafai ake jin labarin hukunci ba.

Akwai dai 'yan kasar China da kamfanoninsu da dama dake harkar ma'adanai a jiohohi da dama na Najeriya.

Masana dai an cewa ba a sai'do da kuma bin ka'ida sosai a harka hakar ma'adanai.

To sai dai kuma hukumomin Najeriya na cewa yanzu sun dukufa domin dakile harkokin hakar ma'aidanai ab bisa ka'ida ba a kasar, domin kare muhallli, da lafiyar jama'a, da bunkasa kudaden shiga na gwamnati da kuma kyautata yanayin aikin leburori wadanda galibi a ke cewa ana ci da guminsu.