Winter Olympics: An hana gina masallaci a Koriya Ta Kudu

A ranar Juma'a ne aka fara gasar Olympics ta hunturu a Koriya Ta Kudu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A ranar Juma'a ne aka fara gasar Olympics ta hunturu a Koriya Ta Kudu

Hukumar kula da harkokin yawon bude ido ta Koriya Ta Kudu KTO, ta soke wani shirin samar da masallacin tafi-da-gidanka da aka yi niyyar samarwa a Gangneung saboda gasar Olymoics ta hunturu, sakamakon kin hakan da masu fafutuka da ke adawa da musulunci suka nuna.

Sashen hukumar na birnin Gangneung ne ya shaida wa kafar yada labarai ta Al Jazeera hakan.

A ranar Juma'a ne aka fara gasar Olympics ta hunturu a Koriya Ta Kudu.

Duk da cewa yawan musulman Koriya Ta kudu kashi 0.2 cikin mutum miliyan 51 na kasar ne, hukumar KTO ta yi niyyar gina wajen sallah ga musulmai a lokacin gasar Olympics ta hunturu, saboda ta samar da yanayin da musulmai za su ji dadin zama a kasar, da kuma kara yawan baki musulmai 'yan yawon bude ido.

Sai dai babban jami'in hukumar Kang Suk-ho, ya shaida wa Al Jazeera cewa sun soke shirin ne bayan kungiyoyi da dama sun soke shi.

"Mun samu adawa sosai daga wasu kungiyoyin addinai kan shirin, sun kuma yi barazanar gudanar da zanga-zanga a yayin gasar ta Olympics,' in ji Mista Suk-ho.

"Mun zauna da su don tattauna amma a karshe dole muka fasa wannan shirin."

Ya kara da cewa ba su tsammaci samun adawa daga kungiyoyin ba.