Yanayin da mata ke shiga yayin renon ciki da haihuwa

Yanayin da mata ke shiga yayin renon ciki da haihuwa

Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakken shirin:

A wannan mako shirin Adikon Zamani ya yi duba ne a kan matsalolin da mata ke fuskanta a bangaren renon ciki a haihuwa.

Bakuwata a wannan makon ita ce wata likitar mata, wadda ita ma uwa ce, Dr Habiba Ibrahim.

Samun ciki na daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci da kan samu mace a rayuwarta.

Abun farin ciki ne, amma wasu matan hakan kan zo musu da tarin matsaloli, kama daga amai da tashin zuciya da sauran ciwuka manya da kanana, a wasu lokutan ma har da ciwukan da kan yi barazanar tafiya da rayuwarsu.

Ni da likitar mun tattauna sosai kan yadda za a iya daukar matakan rage radadin halin da mata kan samu kansu a ciki lokacin rainon ciki.

Samun haihuwa abu ne mai matukar dadi a rayuwa, sai dai a arewacin Najeriya har yanzu ana fama da yawan mace-macen mata da jarirai a sanadin haihuwa, saboda rashin wadatacciyar kula da ba sa samu yayin rainon ciki, musamman ma a karkara.

Muna nukatar neman mafita ga wannan yanayi da mata ke shiga. Wani lokacin sai na ga kamar ba ma daukar yanayin ciki da haihuwa da muhimmanci, bayan kuwa mun san cewa magana ce ta ko a mutu ko a rayu.

Samun da ba abu ne na wasa ba, amma ina mamakin yadda bangaren lafiya ba ya mayar da hankali sosai wajen taimakawa masu ciki da jariran da ake haifa.

Yin awon ciki wanda ke da matukar muhimmanci ya zama kwalele ga mata marasa galihu.

A cewar likitoci, rashin isasshiyar kula na iya jawo wa uwaye da jarirai matsala ko da can gaba ne a rayuwarsu.

Alal misali, wani bincike ya gani cewa uwayen da ke samun isasshiyar kulawa yayin da suke da ciki, sun fi haifar yara masu cikakkiyar lafiya.