Kalli hotunan abun da ya faru a Afirka a makon nan 2 - 8 Fabrairu 2018

Wasu zababbun hotuna na abubuwan da suka faru a Afirka a makon nan.

Two young women are seen ahead of a welcoming ceremony for first year students on February 3, 2018 in Beni.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wasu 'yan mata biyu gabanin wani bikin yi wa dalibai maraba a ranar Asabar a gabashin Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wannan dan gayen ma ya halarci bikin.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Daliban suna shiga shekararsu ta farko ne a karatun jami'a.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An gano wani zanen da mai matukar daraja da wani dan Najeriya Ben Enwonwu ya yi a wani gida a London. Ana kyautata zaton cewa darajar zanen kan iya kai fam dubu 300 idan an sayar da shi a kasuwar gwanjon kayayaki,

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A ranar Alhamis, daruruwan masu zanga-zanga sun taru a wajen ofishin jakadancin Rwanda a birnin Herzeliya na kasar Isra'ila don nuna adawa da sabbin dokokin ci-rani masu tsauri da aka sanyawa 'yan Afirka.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wani ma'aikacin gidan talbijin na NTV a dakin watsa shieye-shiryensu da ke Kenya a ranar Talata, kwana daya bayan da aka amince gidan talbijin din ya dawo da watsa shirye-shiryensa, bayan dakatar da shi na dan lokaci.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A wannan ranar ce tawagar 'yan wasan tseren dusar kankara ta mata ta Najeriya da suka hada da Seun Adigun da Ngozi Onwumere da Akuoma Omeoga da Simidele Adeagbo suka dauki hoto a yayin da ake maraba da bude taron gasar Olympic na hunturu na 2018 a Koriya Ta Kudu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A ranar Asabar, wani mutum na shirin wani bikin ibada na addinin Hindu da aka sani da Hindu Thaipoosam Kavady a kusa da birnin Durban da ke Afirka Ta Kudu...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A cikin shirye-shiryen bikin har da wadanda suka yi wa jikinsu ado da fenti da allurai, suka kuma dauki kwakwa da wasu kayan marmari da fulawa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A wannan ranar dai a Durban, masoya mawakin reggae na Rastafarian sun taru don bikin ranar Bob Marley Earthday.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Haka kuma a ranar Asabar, wata maziyarci tana daukar hoton wani bangon tarihi da aka gano kwanan nan a tsauni na Giza plateau da ke Alkahira na Masar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A ranar Litinin a Afirka Ta Kudu, magoya bayan shugaban jam'iyya mai mulki ta ANC Cyril Ramaphosa suna zanga-zangar neman Shugaba Jacob Zuma ya sauka daga mulki.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A ranar Juma'a, wani mai gadin fadar shugaban kasar Senegal, yana jiran isowar Shugaban Faransa Emmanuel Macron zuwa Dakar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mawakaiya Rihanna da shugaban Faransa sun halarci wani taron neman inganta harkar ilimi a Afirka a Dakar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A wannan ranar ce dai aka yi nasarar ceto dukkan masu hakar ma'adinai 955 da suka makale a Afirka ta Kudu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A ranar Juma'a kuwa, wani mai gadin gidan yari yana tsaye a gaban kurkuku a birnin Casablanca na Morko.

Hotuna daga AFP da Reuters da kuma Getty Images