Kwan halittar mutum na farko da aka kyankyashe a dakin bincike

  • Daga James Gallagher
  • Wakilin BBC na harkar lafiya da kimiyya
scientist

Masu bincike a jami'ar Edinburgh sun ce a karon farko an kyankyashe kwan halittar mutum dakin bincike.

Tawagar masu binciken sun ce kyankyasar zata iya samar da sabbin hanyoyin adana kwan halittar yara da ake yiwa maganin cutar kansa.

Hakan kuma wata dama ce ta binciko yadda kwan halittar dan adam ke girma wanda kawo yanzu masana ilimin kimiyya basu iya ganowa ba.

Kwararru sun ce wannan wani muhimmin ci gaba ne sai dai akwai bukatar kara aiki sosai kafin fara amfani da fasarar a asibitoci.

Ana haihuwar mace da kwayoyin halittar da basu gama girma ba a mahaifar mace kuma kwayoyin na gama cika ne a lokacin da mace ta zama budurwa.

An shafe shekaru da dama ana aiki, amma masana kimiyya zasu iya kyankyashe kwayoyin halittar a wajen mahaifa.

Kyankyasar na bukatar daidaita yanayin numfashi da kwayaye da kuma sinadarin protein mai gina jiki tare da inda ake kyankyashe kwayoyin halittar.

'Abun farin ciki ne'

Sai dai yayin da masana kimiyya ke cewa wannan wani abu ne da zai yiwu na hanyoyin iya kyankyasar kamar yadda mujallar kimiyya ta Molecular Human Reproduction ta rubuta, binciken ya nuna cewa sai an sake tantancewa.

Ba zai zama mai inganci ba kasancewar kashi 10 ne kawai na kwayoyin suke iya kaiwa matakin kyankyasa.

Kuma kwayayen basu gama girma ba, a don haka babu tabbaci ko zasu yi wani amfani.

Daya daga cikin masu binciken, Farfesa Evelyn Telfer, ta shaidawa BBC cewa: "abun farin ciki ne a samu wata shaida data nuna cewa abu ne mai yiwuwa a iya kaiwa wannan mataki game da kwayoyin halittar dan adam.''

Asalin hoton, University of Edinburgh

Bayanan hoto,

Dakin bincike a jami'ar Edinburgh inda masana kimiyya suka kyankyashe kwan halittar dan Adam

Hanyoyi da ake bi wajen kyankyasar suna da tsauri sosai kuma an daidaita su ne da jikin dan adam- wasu kwayaye zasu girma a lokacin dan adam ke karami, wasu kuwa sai bayan shekaru 20.

Ana bukatar sai kwan halitta ya kai wani yanayi tukuna, idan ba haka ba kuma za'a samu kwayoyin halittar da dama a lokacin da maniyyi ke sarrafa shi

Farfesa Telfer na ganin wannan abun damuwa ne, koda yake tana ganin za'a iya shawo kan lamarin ta hanyar inganta fasahar da ake amfani da ita.

A yanzu dai samun iya hada wannan ci gaban da jikin dan adam, zai iya bada dama wajen taimakawa kananan yara dake fama da cutar cancer.