Winter Olympic 2018: Mike Pence ya ki gaisawa da 'yan Koriya Ta Arewa

korea south

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Juma'a ne aka bude gasar wasannin Olympic na Hunturu a birnin Pyeongchang na kasar Koriya ta Kudu.

'Yan wasa daga sassa daban-daban na duniya ne za su shiga, inda a karon farko har da 'yan kasashen yammacin Afrika, wato Ghana da Najeriya.

Haka kuma Koriya ta Arewa ma za ta shiga, wadda take zaman doya da manja da Koriya ta Kudun.

Kafin wannan biki dai an shirya wata liyafar cin abinci, wadda ta samu halartar mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence.

Sai dai rahotanni sun ce bai fi minti biyar a wajen walimar ba, kuma bai zauna ya fuskanci wakiliyar Koriya ta Arewa kuma kanwar Shugaba Kim Jong-Un ba.

Koriya ta Kudu da ta Arewa sun yi yarjejeniyar fafatawa a wasannin Olympics din a matsayin tawaga guda, da fatan cewa hakan zai sassauta takaddamar da ke tsakanin kasashen biyu dangane da shirin nukiliyar Koriya ta arewa tare kuma da yawkaka kawance a tsakaninsu.

Cho Kun-Young, wani mazaunin Koriya ta kudu ne, kuma ya nuna farin cikinsa da halartar wasannin da daya daga cikin 'ya'yan gidan da ke mulkin Koriya Ta Arewa ta yi.

"Ina da kyakkyawan zato game da ziyarar Kim Yo Jong a Koriya ta Kudu. Na kuma yi imani wannan ziyarar za ta bude wata babbar hanya ta kawo ci gaba a dangantakar da ke tsakanin Koriyoyin biyu da kuma wanzuwar zaman lafiya a duniya."

Asalin hoton, Getty Images

Sai dai kuma duk da haka, rahotanni sun nuna cewa kafofin yada labarai na Koriya ta Arewa ba su haska bikin bude gasar ta Olympics ba.

Hasali ma, a lokacin bikin da karfe 11 na safe agogon GMT, wato karfe 7.30 na yamma agogon Koriya Ta Arewan, babban gidan talabijin na kasar wasu wake-wake na kishin kasa ya yi ta sakawa.

A halin da ake ciki kuma, za a ci gaba da wasannin ne ba tare da wasu 'yan wasa da koci-kocin Rasha guda 47 b, wadanda aka yi watsi da daukaka karar da suka yi bayan da a ka hana su fafatawa a wasannin.

Hukuncin ya zo ne sa'o'i kafin a fara bikin bude wasannin a Pyeongchang inda aka haramtawa Rasha fafatawa, saboda wasu 'yan wasan kasar sun sha kwayoyin kara kuzari a wasannin Olympics da aka yi a Sochi a shekarar 2014.