Buhari ya kori wasu alkalai biyu daga aiki

Buhari ya ce gwamnatinsa zata magance cin hanci da rashawa a bangaren shari'a

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Bayanan hoto,

Buhari ya ce gwamnatinsa zata magance cin hanci da rashawa a bangaren shari'a

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kori wasu alkalai na babbar kotun tarayya daga aiki.

Wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ta ce an kori mai shari'a O.O Tokode na babbar kotun tarayya dake Benin.

Sanarwar ta ce shugaba Buhari ya kuma yiwa mai shari'a A. F. A Ademola ritaya daga aiki a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Sanarwar ta kara da cewa shugaban kasar ya dauki matakin korar alkalan ne bayan ya amince da shawarwarin da hukumar kula da alkalai ta kasar ta gabatar masa.

Shugaba Buhari ya ce daga yanzu sai alkalan da suka cancanta ne kawai zasu rika shari'a a kotunan kasar.