Jirgi ya kashe mai daukar hoton 'selfie'

Jirgin kasa ya kade mai daukar hoton selfie har lahira a Thailand

Asalin hoton, LILLIAN SUWANRUMPHA

Bayanan hoto,

Jirgin kasa ya kade mai daukar hoton selfie har lahira a Thailand

Wani jirgin kasa ya yi sanadin ajalin wata mata da take daukar hoton selfie tare da abokinta a Thailand.

Abokin matar ya ce, bayan sun dan yi shaye-shayensu, sai suka yanke shawara cewa yakamata su dauki hoto a kusa da wani jirgin da ke tsaye.

'Yan sanda sun ce suna cikin daukar hoton na selfie ne ba su ankara da tahowar wani jirgi daga daya layin dogon ba, sai kawai ya buge su.

Matar mai kimanin shekara 24 da haihuwa, ta ji munanan raunuka a kafarta inda ta mutu bayan an kai ta asibiti, yayin da shi kuma abokin nata ya samu raunuka, amma bai mutu ba.

Wannan lamari dai ya faru ne a tashar jirgin kasa ta Samsen, da ke Bangkok.

Ana dai samun karuwar mutuwar mutane a lokacin da suke daukar hoton selfie a wurare daban-daban na duniya.

Ko a watan daya gabata, sai da wani jirgin kasa a Hyderabad ya kade wani mai daukar hoton selfie, lamarin da ya sa ya samu munanan raunuka.

Daukar hotuna a lokutan da jirgin kasa ke tahowa, ya zamo wani abu na ya yi da ke da matukar hadari a wasu kasashen duniya.