Har yanzu zabiya da masu sanko na fuskantar barazana

Masafan sun yi ammanar cewa akwai zinari a cikin kan ma su sanko

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masafan sun yi ammanar cewa akwai zinari a cikin kan ma su sanko

Shugaban hukumar yan sanda a Mozambique , Bernadino Rafael, ya yi kira ga yan kasar akan su rika sa ido tare da ankarar da jamian yan sanda kan masu aikata miyagun laifuka musaman masu kashe zabiya da maza masu sanko.

Ya ce akwai wasu mutane da basu da aikin yi ,illa neman zabiyar da zasu kashe saboda zargin da ake yi akan cewa akwai sasan jikinsu da masafa ke amfani da su domin azurta wasu.

Mr Rafael ya kuma ce wasu bata gari sun ce akwai zinari a cikin kan masu sanko.

Mr Rafael din ya bayyana haka ne a a taron gangamin da aka yi a garin Massinga da ke kudanci inda ya jadada muhimanci sa ido kan abubuwa da ke faruwa a cikin alumma.

Sai dai ya yi kira ga mutane akan su daina daukar doka da hannunsu akan wadanda ake tuhuma da aikata ba dai dai ba ta hanyar cina mu su wuta .

Ya ce mafi alheri shine a mika wand aka kama ga hukumomi domin ayi masa tambayoyi.