Ana zaben kananan hukumomi a jihar Kano

Sama da jam'iyyu ashirin ne ke fafatawa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sama da jam'iyyu ashirin ne ke fafatawa a zaben

A ranar Asabar ne aka zaben kananan hukumomi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Kano na da kananan hukumomi 44, fiye da kowacce jiha a kasar.

Shugaban hukumar zaben jihar, Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya shaida wa BBC cewa jam'iyya sama da ashirin ne ke fafatawa a zaben.

Sai dai masu sharhi na ganin jam'iyyar APC mai mulkin jihar bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ce za ta yi kidanta ta kuma yi rawarta.

Jam'iyyar PDP da ke hamayya ba ta shiga zaben ba saboda, a cewarta, kudin fom din da aka sayarwa 'yan takara ya wuce kima.

Shugaban jam'iyyar Sanata Mas'ud El-Jibril Doguwa ya gaya wa BBC cewa "za mu garzaya daga nan har kotun koli domin ganin an yi mana adalci", bayan karamar kotu ta kori karar da suka shigar a kan batun.

Ana gudanar da zaben ne a daidai lokacin da Gwamna Ganduje ke tsaka da rikicin siyasa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, mutumin da ya goyi bayansa wurin yin nasarar zabe a shekarar 2015.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

PDP ta garzaya kotu inda take kalubalantar zaben