Shin 'yan majalisa na shirin yi wa Buhari wayo a zaben 2019 ne?

Shin 'yan majalisa na shirin yi wa Buhari wayo a zaben 2019 ne?

Latsa alamar lasipika domin sauraren tattaunawa da Honourable Mohammed Soba

Majalisun dokokin tarayyar Najeriya sun ce sun sauya fasalin tsarin zaben 2019 ne domin Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya samu damar sanya ido a zabukan.

Shugaba Buhari bai ce zai sake tsayawa takara a zaben 2019 ba tukunna.

A gyaran da 'yan majalisun suka yi wa tsarin zaben, za a soma ne da zaben majalisar dokokin tarayya kuma zaben shugaban kasa ne zai zo a karshe.

Wasu 'yan kasar sun soke su kan hakan, suna masu cewa matakin tamkar wata dama ce ga 'yan majalisar su lashe nasu zaben sannan su yi watsi da shugaban kasa.

Sai dai dan majalisa Mohammed Musa Soba ya shaida wa BBC cewa "mun dauki matakin ne domin mu bai wa shugaban kasa damar sanya ido kan zabukan da za su zo kafin nasa."