Syria ta harbo jirgin yakin Isra'ila

Crash site of an Israeli F-16 jet in northern Israel. Photo: 10 February 2018

Asalin hoton, Reuters

Rundunar sojin Isra'ila ta ce jirgin yakinta samfurin F-16 ya fado lokacin da dakarun Syria suka bude masa wuta a yayin da yake shirin kai hari kan yankunan Iraniyawa a kasar.

Matukan jirgin biyu sun yi nasarar fita daga cikinsa ta hanyar amfani da lema kafin ya fadi a arewacin Isra'ila. An yi amannar cewa wannan ne karon farko da jirgin Isra'ila ya fado sakamakon rikicin na Syria.

Gwamnatin Isra'ila na kai hare-hare ne bayan Iran ta kaddamar da aike wa da jirgi maras matuka cikin Isra'ila.

An dai kama jirgin.

Kafafen watsa labarai sun ce Syria ta bude wuta ne bayan Isra'ila ta yi mata "kutse".

Wakilin BBC a Gabas Ta Tsakiya Tom Bateman ya ce hare-haren da Isra'ila ke kai wa Syria ba sabon abu ba ne, amma faduwar jirginta zai ta'azzara al'amura.

Daga bisani rundunar sojin Isra'ila ta ce tana yin raddi ta hanyar kai manyan hare-hare kan Iraniyawa da ke kasar.

Ma'aikatar tsaron Isra'ila ta aike da sakon Twitter da ke cewaIsrael Defense Forces (IDF) tweeted: "Dazun nan jiragenmu suka kai hari kan tsarin tsaron Syria da Iran da ke Syriar. An kai harin ne kan wurare 12, ciki har da hare-hare ta sama uku da kuma hari hudu kan sojojin Iran. An harbo makamai masu linzami da ke kakkabo jiragen sama kan Isra'ila, lamarin da ya sa muka karfafa tsaro a arewacin Isra'ila."