Mai taimakawa Trump ya ajiye aiki saboda 'ci zarafin' matarsa

Trump official David Sorensen

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

David Sorensen ne ke rubutawa Shugaban Amurka Donald Trump jawaban da zai gabatar

Mutumin da yake rubutawa Shugaban Amurka Donald Trump jawabai ya zama mataimakinsa na biyu da ya sauka daga mukaminsa a wannan makon saboda zargin cin zarafin matarsa.

David Sorensen ya musanta zargin da tsohuwar mai dakinsa ta yi cewa ya sha cin zarafinta.

Ajiye aiki ne kwana biyu bayan wani mai taimakawa Mr Trump, Rob Porter, ya sauka daga mukaminsa saboda zargin da tsoffin matansa biyu suka yi masa na cin zarafinsu, ko da yake ya musanta zargin.

Ana ta tambaya kan lokacin da fadar White House za ta dauki mataki game da zarge-zargen da aka yi wa Mr Porter.

Tsohuwar matar Mr Sorensen Jessica Corbett ta shaida wa jaridar the Washington Post cewa ya ci zarafinta lokacin da suka yi aure.

Ta kara da cewa sau da dama tsohon mijin nata yana hawa kan kafafunta da motarsa, sannan ya tura ta a jikin bango ko kuma ya kashe wutar taba sigari a hannunta.

Sai dai wata sanarwa da Mr Sorensen ya fitar ta ce bai "taba cin zafarin kowacce mace ba daukacin rayuwarsa", yana mai cewa hasalima shi ne aka ci zarafinsa.

Ya kara da cewa ya duba yiwuwar kai tsohuwar matar tasa kara a kotu amma ya fasa saboda ba ya son "mutuncin fadar White House ya zube".