Ba wajibi ne matan Saudiyya su sanya abaya ba - Malami

Saudi women wearing the abaya at a camel festival

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto,

Dokar kasar ta umarci mata su ringa sanya abaya

Wani babban Malamin addinin Musulinci a Saudiyya ya ce ba wajibi ne matan kasar su rika sanya abaya domin rufe jikinsu a bainar jama'a ba.

Sheikh Abdullah al-Mutlaq, wanda mamba ne a Majalisar manyan Malaman kasar, ya bukaci mata su ringa shiga ta kamala, amma ba sai sun sanya abaya ba.

A yanzu dai dokokin Saudiyya sun bukaci mata su rika sanya abayar.

Malamain ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da ake sauya dokokin kasar da kuma sassauta wasu hukunce-hukunce masu tsauri da aka yi kan mata.

"Fiye da kashe 90 na matan Musulmi muminai a fadin duniya ba sa sanya abaya. Don haka bai kamata mu tilasta sanya ta ba," in ji Sheikh Mutlaq.

Wannan ne karon farko da wani babban Malami ya yi kalami irin wannan.

Kalaman Sheikh Mutlaq sun jawo zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta, inda wasu ke goyon bayansa yayin da wasu ke tur da su.

"Sanya abaya wata al'adace a wannan yanki namu kuma kowa yana yin hakan. Ba magana ce ta addini ba," in ji wani mai amfani da shafin Twitter Mashari Ghamdi.

"Ko da sau dari aka bayar da fatwa kan kada a sanya abaya, na rantse ba zan daina amfani da ita ba har karshen rayuwata. Ina kira ga mata da kada su daina amfani da abaya..." in ji wata mai shafin Twitter @Kooshe90.

A shekarar 2016, an daure wata 'yar kasar Saudiyya saboda ta cire abayarta a kan titin birnin Riyadh, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto,

A watan jiya ne aka bar mata su shiga filin wasa domin kallon wasan kwallon kafa