Boko Haram: Najeria za ta ci gaba da yi wa wadanda ta kama shari'a

Mayakan Boko Haram

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta ci gaba da yi wa 'ya'yan kungiyar Boko Haram da aka kama shari'a.

Wata sanarwa da kakakin ministan shari'ar kasar Abubakar Malami, Salihu Othman Isah, ya aikewa manema labaria ta ce za a ci gaba da zagaye na biyu na shari'ar da ake yi wa 'yan Boko Haram din ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairu a cibiyar tsare mutane ta Kainji da ke jihar Naija.

"Za a ci gaba da yi musu shari'a ne bayan an kammala bincike kan 'yan kungiyar fiye da dubu daya da kotu ta bayar da umarni a yi musu bincike a zamanta na watan Oktoba na shekarar 2017," in ji sanarwar.

A cewar ministan, za a yi shari'ar wadanda aka tabbatar da kwararan shaidun aikata ta'addanci a kansu, yayin da za a sallami mutanen da aka gano ba su da hannu wajen kai hare-hare.

"Kazalika za a mika wadanda aka amince a sallama ga ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha'anin tsaro domin a sauya musu tunanin tayar da kayar bayan da suke da shi, sannan a sake su.

"Za a saki wasu daga cikin mutum 468 da ake zargi da kasance mambobin kungiyar saboda babu wata shaida da ke nuna su 'yan kungiyar ne, sannan za a mika su a hannun ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha'anin tsaro daga cikin mutum 1669 da ake tsare da su a Kainji," in ji ministan.

Ya kara da cewa za a ba da dama ga kungiyoyin farar hula da 'yan jarida su halarci shari'ar.

Wannan dai shi ne karo na biyu da ake yi wa 'yan kungiyar ta Boko Haram da aka kama shari'a a cibiyar tsare mutane ta Kainji.

Sai dai a wancan lokacin ba a bar 'yan jarida sun jalarci zaman ba.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta saki wasu malaman Jami'ar Maiduguri da kuma 'yan sanda da mayakan kungiyar suka tsare a shekarar 2017.