Boko Haram ta saki malaman jami'ar Maiduguri

Boko Haram ta sace malaman ne lokacin da suke aiki a tafkin Chadi

Asalin hoton, Premuim times

Bayanan hoto,

Boko Haram ta sace malaman ne lokacin da suke aiki a tafkin Chadi

Gwamnatin Nigeria ta ce Boko Haram ta sako mutane 13 da suka hada malaman jami'ar Maiduguri da kuma wasu matan 'yan sanda.

A cikin wata sanarwa da ke dauke da sa hannun kakakin shugaban kasa Malam Garba Shehu, ta ce hukumar tsaro ta farin kaya ta yi wa shugaba Muhammadu Buhari bayani kan yadda aka sako mutanen.

Ta ce a ciki akwai malaman jami'ar Maiduguri nan su 3 da kuma wasu matan 'yan sanda 10 da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi garkuwa da su.

Sanarwar ta ce an sako mutanen ne sakamakon jerin tattaunawar da hukumomin kasar suka rika yi da 'yan Boko Haram din, karkahsin jagorancin kungiyar agaji ta Red Cross.

Gwamnatin Nigeriya ta ce dukkanin mutanen su 13 na hannun hukumar ta DSS kuma suna kan hanyarsu ta zuwa Abuja.

Sanarwar ta ce an ajiye likitoci da kuma masana masu nazari kan hallayar bil' adama domin basu kulawar da ta kamata idan sun iso helkwatar hukumar da ke Abuja.

Watakila a gabartawa shugaban kasa da mutanen idan babu wata damuwa kan tsaron lafiyarsa da kuma lafiyarsu, daga bisani kuma a mikasu ga iyalansu.

Mayakan Boko Haram sun sace malaman jami'ar Maidugurin ne lokacin da aikin neman man fetur a tafkin Chadi a garin Magumeri da ke jihar Borno.

Boko Haram sun yi awon gaba da matan ne lokacin da suka hari kan wani ayarin motoci na sojoji da kuma yan sanda a hanyar Damboa da ke kusa da garin Maiduguri.