APC ta lashe dukkan zaben kananan hukumomin jihar Kano

Gwamna Ganduje yayin da yake kada kuri'a

Asalin hoton, KANO STATE GOVERNMENT

A Najeriya jam`iyyar APC mai mulki ta lashe baki dayan kujerun shugabanni da kansiloli a kananan hukumomin jihar Kano arba`in da hudu.

Jam`iyyun siyasa 25 ne suka shiga zaben, ban da jam`iyyar adawa ta PDP wadda ta kaurace masa.

Sai dai wasu kungiyoyin farar-hula sun bayyana cewa an yi jinkiri sosai wajen fara zaben, suna kuma zargin an tabka magudi.

Kazalika wasu rahotanni sun nuna cewa ba a fito sosai wurin kada kuri'a ba.

Dr Mohammed Mustapha na kungiyar Democratic Action Group ya shaida wa BBC cewa zaben tamkar yi wa dimokuradiyya karan-tsaye ne.

A cewarsa, "Har karfe biyu ba a kawo kayan aiki ba, babu ma'aikata. Wannan yi wa dimokaradiyya kanshin mutuwa ne kuma gazawa ce ga hukumar zaben jihar Kano da kuma gwamnatin jihar.

"Ban taba ganin zaben da bai yi armashi ba irin wannan; kuma hakan na nuna cewa idan aka bai wa jihohi dama su kafa wasu hukumomi ba za su yi adalci ba."

Sai dai hukumar zaben jihar Kano a nata bangaren ta ce ba da gangan ta yi jinkirin ba.

"An samu jinkiri ne ba don muna so ba, sai don jirgin da zai kawo kayan bai zo da wuri ba," in ji wani baturen zabe a karamar hukumar Bebeji.

'PDP da Kwankwaso ba su shiga zaben ba'

Jam'iyyar PDP da ke hamayya ba ta shiga zaben ba saboda, a cewarta, kudin fom din da aka sayar wa 'yan takara ya wuce kima.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

PDP ta garzaya kotu inda take kalubalantar zaben

Shugaban jam'iyyar Sanata Mas'ud El-Jibril Doguwa ya gaya wa BBC cewa "za mu garzaya daga nan har kotun koli domin ganin an yi mana adalci", bayan karamar kotu ta kori karar da suka shigar a kan batun.

An gudanar da zaben ne a daidai lokacin da Gwamna Ganduje ke tsaka da rikicin siyasa da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, mutumin da ya goyi bayansa wurin yin nasarar zabe a shekarar 2015.

Bangaren tsohon gwamna Kwankwaso ma bai shiga zaben ba.