Mun ji dadin sako abokan aikinmu - Malaman Jami'ar Maiduguri

Malaman Jami'ar Maiduguri

Asalin hoton, PREMUIM TIMES

Kungiyar Malaman Jami'a reshen Jami'ar Maiduguri ta bayyana matukar jin dadinta saboda sakin mambobinta da kungiyar Boko Haram ta yi.

Wata sanarwa daga fadar gwamnatin Nigeria ta ce an sako mutane 13 da suka hada malaman Jami'ar Maiduguri da kuma wasu matan 'yan sanda ranar Asabar.

Shugaban kungiyar Malaman Jami'ar reshen Jami'ar Maiduguri, Dr Mamman Dani, ya shaida wa BBC cewa su baki har kunne dangane da sako abokan aikin nasu.

"Alhamdulillahi, mun yi murna kwarai da gaske kuma muna gode wa Ubangiji da ya sa aka sako wadannan mutanen namu. Ba mu samu mun tattauna da su ba tukunna, amma mun yi waya da iyalansu da sauran abokan arziki," in ji shi.

Ya kara da cewa iyalan Malaman Jami'ar da aka sako "suna cikin murna kamar yadda mu ma muke cikin murna."

A watan Yunin shekarar 2017 aka sace Malaman, wadanda ke yi wa babban kamfanin mai na Najeriya, NNPC bincike kan tarin albarkatun mai a yankin Tafkin Chadi.

An yi awangaba da mutanen ne bayan wani kwantan bauna da aka yi musu a kusa da kauyen Jibi da ke jihar Borno.