Jirgin Rasha ya yi hadari da fasinjoji 71 a Moscow

Asalin hoton, AIR TEAM IMAGES
Jirgin bai kai shekaru takwas da aka saye shi ba
Wani jirgin sama dauke da fasinjoji 71 ya fadi jim kadan bayan tashi a filin jirgin sama na Domodedovo a birnin Moscow na kasar Rasha.
Jirgin saman na kamfanin Saratov ya bace ne bayan tashin sa inda ya fado kusa da kauyen Argunovo mai nisan kilomita 80 daga arewa maso gabashin Moscow.
Jami'ai sun shaidawa kafofin watsa labarai na Rasha cewa ana kyautata zaton daukacin fasinjoji 65 da ma'aikatan jirgin 6 sun mutu.
Jirgin kirar-148 na kan hanyarsa ce ta zuwa birnin Orsk kusa da kan iyakar Rasha da Kazakhstan kuma ya fado ne da tsakar rana.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya mika ta'aziyarsa ga iyalan wadanda ke cikin jirgin inda ya umurci a gudanar da bincike kan musabbabin hadarin.
Hotunan da aka dauko sun nuna tarkacen jirgin kankara ta lullube a a kudu maso gabashin Moscow.
Asalin hoton, Reuters
Hotunan da aka dauko sun nuna tarkacen jirgin kankara ta lullube a kudu maso gabashin Moscow
Kamfanin dillancin labarai na Tass News ya ambato wani jami'i na cewa an gano gawar wasu mutane kusa da wurin da aka yi hadarin.
Kamfanin sufurin jirgin sama na Saratov Airlines yana garin Saratov, mai nisan kilomita 840 kudu maso gabashin Moscow.
A shekarar 2015 an dakatar da jiragen kamfanin daga tafiye tafiye zuwa kasashen waje bayan da masu bincike suka ga wani mutum da ba ma'aikacin jirgi ba dakin da matuka jirgi ke aiki.
Sai dai kamfanin ya daukaka kara kan dakatar da shi zirga-zirga zuwa kasashen waje inda kuma ya sauya tsare tsaren sa kafin a bari a rika dauakr jiragen kamfanin shata zuwa kasashen waje a 2016.
Jiragen kamfanin dai na zirga-zirga ne tsakanin biranen Rasha da kuma wasu garuruwa a Armenia da Georgia.