Jirgin Rasha ya yi hadari da fasinjoji 71 a Moscow

Hotunan da aka dauko sun nuna tarkacen jirgin kankara ta lullube a kudu maso gabashin Moscow

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Hotunan da aka dauko sun nuna tarkacen jirgin kankara ta lullube a kudu maso gabashin Moscow

Wani jirgin sama dauke da fasinjoji 71 ya fadi jim kadan bayan tashi a filin jirgin sama na Domodedovo a birnin Moscow na kasar Rasha.

Jirgin saman na kamfanin Saratov ya bace ne bayan tashin sa inda ya fado kusa da kauyen Argunovo mai nisan kilomita 80 daga arewa maso gabashin Moscow.

Jami'ai sun shaidawa kafofin watsa labarai na Rasha cewa ana kyautata zaton daukacin fasinjoji 65 da ma'aikatan jirgin 6 sun mutu.

Jirgin kirar-148 na kan hanyarsa ce ta zuwa birnin Orsk kusa da kan iyakar Rasha da Kazakhstan kuma ya fado ne da tsakar rana.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ma'aikatan agaji sun isa wurin da jirgin ya fado

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya mika ta'aziyarsa ga iyalan wadanda ke cikin jirgin inda ya umurci a gudanar da bincike kan musabbabin hadarin.

Hotunan da aka dauko sun nuna tarkacen jirgin kankara ta lullube a a kudu maso gabashin Moscow.

Kamfanin dillancin labarai na Tass News ya ambato wani jami'i na cewa an gano gawar wasu mutane kusa da wurin da aka yi hadarin.