Hukumar NAPTIP ta rufe asibitin da ake sayar da jarirai a Abuja

An sha samun gidajen da ake sayar da jarirai a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An sha samun gidajen da ake sayar da jarirai a Najeriya

Hukumar hana safarar mutane a Najeriya NAPTIP ta ce ta rufe wani asibitin gargajiya da take zargin ana haihuwa tare kuma da sayar da jarirai a Abuja.

Wata sanarwa da kakakin hukumar Mr Josiah Emerole ya aikewa manema labaru, ta ce rufe asibitin gargajiyar mai suna Akuchi Herbal Concept wani bangare ne na ci gaba da bincike da hukumar ke yi kan zargin sayar da jarirai a asibitin.

Hukumar ta ce tun a wasu makonni ne aka kame Mr. Chigozie John Emmanuel da ake yiwa lakabi da suna Akuchi a asibitinsa dake unguwar Nyanya, Abuja.

Sanarwar ta kara da cewa jami'an NAPTIP sun kuma gano wasu magungunan gargajiya wadanda mutumin da ake zargi ya ce yana amfani da su wajen kara yawan kwayayen haihuwa ga mata.

Ana dai zargin sa ne da damfarar wasu mata akan cewar sun samu juna biyu bayan sun nuna cewa suna matukar bukatar jarirai.

Daga bisani sai ya basu jarirai na wasu mutane dabam inda yake karbar makuden kudade a hannun matan.

Sanarwar ta kara da cewa an kame mutamin ne bayan 'yan sanda a Abuja sun kama wata mata da jariri akan hanyarta ta zuwa garin Minna na jihar Niger.

Daga bisani matar ta shaidawa 'yan sanda cewa tana zuwa asibitin Mr. Emmanuel inda ya rika bata wasu magunguna kasancewar ta shafe shekaru bata samu haihuwa ba.

A cewar kakakin hukumar ta NAPTIP, zargin sayar da jarirai a asibitin ya ja hakulan 'yan Nigeria da dama musamman 'yan uwan wasu dake zuwa asibitin gargajiyar.

Hukumar ta ce tana ci gaba da bincike don gano duk wani dake da hannu wajen safarar jarirai a asibitin dama wasu wurare a kasar.

A baya dai Matsalar sayen da jarirai matsala ce da aka fi samunta a wasu yankuna na kudancin Nigeria.

Sai dai a 'yan kwanakin nan ana ta samun karuwar matsalar gidajen da ake zargi ana sayar da jarirai a wasu sassa na arewacin kasar.

A watan Janairun 2018 ma gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da rufe wasu gidajen marayu da tace ana amfani dasu wajen sayar da jarirai.