Matan Boko Haram na tsaka mai wuya

Nigerian soldier on guard duty in Damasak north-eastern Nigeria

A shekarar da ta gabata kungiyar Boko Haram ta yi amfani da 'yan kunar bakin wake yawanci mata fiye da duk wata kungiyar ta'addanci.

Kungiyar na tura matasan 'yan mata kusan a duk mako domin kai harin kunar bakin wake a kasuwanni da masallatai kai hatta ma da sansanonin 'yan gudun hijira.

Akwai kuma dubban irin wadannan mata matasa da suke rike da su a sansanoninsu inda suke tilasta musu auren mayakansu.

A kwanan nan wasu da yawa daga cikin matan sun samu damar tserewa daga hannun 'yan Boko Haram din.

Stephanie Hegarty ta BBC ta je Maiduguri babban birnin jihar Borno cibiyar kungiyar ta 'yan Boko Haram, inda ta gana da wasu daga cikin matan da suka tsira.

Wakiliyar ta gano cewa matan da suka tsirar na cikin wani yanayi na gaba kura baya sayaki; duk da cewa sun tsere daga hannun 'yan Boko Haram to amma kuma a gida suna fuskantar kyama saboda kasancewa a hannun masu tayar da kayar bayan.

Kamar yadda lamarin ya shafi wata mai suna Fatima, wadda matashiya ce mai shekara 19, kuma tana zaune da iyayenta a birnin Maiduguri ne.

Haduwarta da 'yan kungiyar Boko Haram sun fara ne bayan ta kammala makarantar Islamiyya tana shirin samun miji domin ta yi aure ta ci gaba da rayuwarta.

Sai kwatsam wannan kaddara ta fada mata a lokacin da ta kai ziyara garin kakanninta, lokacin da mayakan Boko Haram suka kai hari garin.

Wanna abin ya bude wani sabon babi a rayuwarta.

Daga nan ne mayakan suka yi awon gaba da Fatima, suka kai ta wani sansaninsu, inda suka tilasta mata auren wani daga cikin mayakan, haka ta ci gaba da rayuwa da shi.

Abinka da rayuwa da tayar da kayar baya, a kwana a tashi mijin nata ya gamu da ajalinsa.

Daga na sai Fatima ta sha damarar bama-bamai na kunar bakin, ta kama hanyar zuwa birnin da ta girma, kamar yadda aka tura ta, ta kai harin da zai halaka ta da sauran jama'a masu kan uwa da wabi. Amma kuma a zuciyarta burinta a lokacin shi ne ta tsira daga hannun 'yan Boko Haram din

Da dama ga irin wadannan 'yan mata, tsira daga hannun 'yan Boko Haram ba shi ne karshen wannan rayuwa mai tayar da hankali ba, domin kamar sun gudu ne ba su tsira ba.

Wannan ne halin da suke samun kansu a ciki, daga bisani, domin, komawarsu cikin al'umma da iyalinsu, sai kuma su ga kusan ba a maraba da su, ana musu kallon kusan ba su da bambanci da 'yan Boko Haram.

Abin ma ya fi tsanani ga wadanda aka tilasata wa zuwa kai harin kunar bakin wake.

Bayan duk wannann abu da ya faru da ita wanda yake kamar mafarki, a yanzu Fatima na ganin ta taki sa'a a rayuwarta da ta fito daga waccan rayuwa a hannun 'yan Boko Haram.

A karshe dai Fatima ta kasance daya daga cikin matasan 'yan mata wadanda suka yi sa'ar dawowa su ci gaba da rayuwarsu da sauran jama'a bayan kasancewa tare da 'yan Boko Haram.