Mo Ibrahim: Ellen Johnson Sirleaf ta lashe $5m

Liberia Ellen Johnson Sirleaf

Asalin hoton, Getty Images

Tsohuwar shugabar kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf ce ta lashe lambar girma ta Mo Ibrahim, da ake bai wa shugaba na gari a nahiyar Afirka, kuma lambar yabon ta hada da kudi dala miliyan biyar.

Misis Sirleaf ta kasance mace ta farko da ta zama shugabar wata kasa a Afirka a 2006, kuma a watan jiya ne ta sauka daga mukamin.

Ana yaba ma ta a fagen kokarin hada kan al'ummomin kasar bayan yakin basasar da ya daidaita kasar.

Kwamitin da ke zabar shugaban da ya fi cancanta ya lura cewa masu sukar lamirin Missi Sirleaf din suna zarginta da kau da kai yayin da cin hanci da rashawa ke habaka a karkashin mulkinta.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaban gidauniyar Mo Ibrahim

An kuma zarge ta da nada na kusa da ita a manyan mukamai, kamar yadda ta ba 'ya'yanta mukamai a gwamnatinta.

Amma kwamitin ya ce ta cancanci lashe wannan lambar yabon na bana saboda yadda ta jajirce wajen jagorantar jama'ar kasar a wani mayuwayacin lokaci.

Misis Sirleaf ta shafe shekaru goma tana mulkin kasar ta Liberia.

Shi kuwa Mo Ibrahim, wanda ya kafa gidauniyar a 2007 da ta ke bada wannan lambar yabon ga shugabannin da suka cancanci yabo, dan asalin kasar Sudan ne wanda ke rike da fasfon kasar Birtaniya.

An dai shirya cewa za a rika bayar da wadannan kudadn a kowace shekara ne, amma a karo shida ba a iya samun shugaban da ya cancanta ba.