Israel ta gargadi Iran bayan ta kai hare-hare a Syria

Hezbollah supporters rallied in the area of Fatima's Gate in Kfar Kila on the Lebanese border with Israel on 10 February 2018 to celebrate the crashing of the Israeli air jet
Bayanan hoto,

Magoya bayan kungiyar Hezbollah sun rika nuna farin cikinsu da harbo jirgin yakin na Isra'ila a gaban sojin Majalisar Dinkin Duniya.

Shugaban Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce kasarsa za ta kare kanta daga abin da ya kira "dukkan hare-hare" bayan da ta kai wasu jerin hare-haren a wasu wurare dake cikin kasar Syria.

Isra'ilar ta kai hare-haren ne bayan da ta ce ta dakile wani hari da aka akai mata da jirgin sama mai sarrafa kansa ta kan iyakar Syria da kasar ta Isra'ila.

Iran ta musanta zargin.

Matuka jirgin sun sami kubuta da rayukansu amma akwai rahotannin da ke cewa an kai su asibiti.

Ana ganin wannan ne karo na farko tun 2006 da Isra'ilar ta rasa jirgin yakinta ta fagen daga.

Bayanan hoto,

Bangaren wani bam mai linzami a kusa da wurin da aka harbo jirgin f-16 din a arewacin Isra'ila

Mista Netanyahu ya ce Isra'ila ba za ta amince da duk wani yunkuri da Iran za ta yi ba domin ta fadada ikonta na soji a Syria.

Amma ya kuma ce kasar Isra'ilar na bukatar "zaman lafiya da makwabtanta", a yayin wata ganawa da ya yi manyan hafsoshin sojin kasar.

Bayanan hoto,

Magoya bayan kungiyar Hezbollah sun rika nuna farin cikinsu da harbo jirgin yakin na Isra'ila a gaban sojin Majalisar Dinkin Duniya.