South Africa: Jami'an ANC za su yanke hukunci akan shugaba Zuma

Supporters of ANC president Cyril Ramaphosa chant slogans outside party headquarter in Johannesburg, on February 5, 2018
Bayanan hoto,

Shugaban jam'iyyar ta ANC Cyril Ramaphosa ya ce wannan batun na "janyo rarrabuwar kawuna"

Ana sa ran manyan jami'an jam'iyya mai mulki ta ANC a Afirka ta Kudu za su nemi shugaba Zuma da ya sauka daga mukaminsa a lokacin wani .

Wakilin BBC a nahiyar Afirka ,Andrew Harding ya ruwaito cewa babban kwamitin jam'iyyar za nemi shugaban da ya yi murabus.

Shugaban jam'iyyar ta ANC, Cyril Ramaphosa ya ce wannan batun na "janyo rarrabuwar kawuna".

Mista Zuma mai shekara 75 na fuskantar tuhume-tuhumen cin hanci da rashawa bayan ya shafe shekaru tara a kan karagar mulki.

"Mun san kuna bukatar a warware wannan batun cikin sauri", inji Mista Ramaphosa a yayin da yake ganawa da wasu mutane a lokacin bikin tunawa da cika shekara 100 da haihuwar marigayi Nelson Mandela, tsohon shugaba kasa kuma bakar fata na farko a kasar.

Masana sun ce idan babban kwamitin jam'iyyar ya nemi Mista Zuma ya sauka, lallai ba shi da zabi illa yayi hakan.