Nigeria: Kun taba jin maciji ya hadiye naira miliyan 36?

Rahotanni sun ce an tara kudin ne daga sayar da katin da ake duba sakamakon jarrabawa. Hakkin mallakar hoto Getty Images

Masu amfani da shafukan zumunta a Najeriya sun yi ta arashi da suka kan yadda wata ma'aikaciyar hukumar tsara jarrabawar shiga jami'a JAMB, ta ce maciji ya hadiye naira miliyan 36 na hukumar, reshen jihar Benue.

Ita dai Philomina Chieshe ta yi ikirarin cewa wani "hatsabibin maciji" ya shiga ofishin hukumar inda ya je wurin da ake ajiye kudi ya hadiye naira miliyan 36.

Rahotanni sun ce an tara kudin ne daga sayar da katin da ake duba sakamakon jarrabawar ta JAMB.

Wata majiya a JAMB ta tabbatar wa BBC cewa an dakatar da matar, sannan an kaddamar da bincike kan yadda "maciji ya hadiye kudin."

Hukumar EFCC, wadda ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, ta aike da sakon Twitter inda take cewa ba za ta yi rahama ga macijin da ke hadiye kudi ba."

#TheEagle shows no mercy for money-swallowing snake(s).

Tuni wasu mutane suka bude shafin Twitter mai suna Macijin Nigeria, wanda ke aikewa da sakonnin arashi kan batun.

Kazalika masu amfani da shafukan zumunta sun yi ta bayyana mamaki game da yadda micijin ya hadiye miliyoyin naira.

Wale Adetona ya ce: "Wanne irin maciji ne zai shiga ofishin JAMB ya hadiye naira miliyan 36 ba tare da ya sari mai gadi ko ma'aikacin ofishin ba?

"Ina mamaki kan yadda micijin da ke jin yunwa ya je ofishin JAMB domin yin rijistar jarrabawa amma maimakon hakan ya hadiye naira miliyan 36 daga ofishinsu da ke Makurdi", in ji Mr Aye Dee.

BBC ta yi ta kokarin jin ta bakin hukumar EFCC kan ko zuwa yanzu wanne mataki ta dauka kan wannan batu, amma har zuwa lokacin rubuta wannan labari ba ta same su ba.

A Najeriya dai an sha samun yanayi daban-daban da kudin gwamnati ke yin batan dabo, amma a iya cewa wannan ne karo na farko da aka taba zargin wata dabba da dauke kudi.

Labarai masu alaka