'Yadda ake cin zarafin mata a gaban Ka'aba'

Muslim people performing Hajj ritual Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mata Musulmi sun bayyana matukar kokawarsu kan yadda ake cin zarafinsu a gaban dakin Allah a lokutan aikin Hajji.

Suna yin amfani da maudu'in #MosqueMeToo da ke aikewa da sakonni kan yadda ake cin zarafin mata a wuraren ibada.

Fitacciyar 'yar jaridar nan 'yar kasar Masar da ke Amurka Mona Eltahawy, ta bayyana yadda wasu suka rika neman yin lalata da ita a lokacin aikin Hajjin shekarar 2013.

Musulmi maza da mata sun soma yin amfani da maudu'in a fadin duniya a ranar Lahadi kuma cikin kasa da sa'o'i 24 an aike da sakon Twitter 2,000 a kan batun.

Ya kasance daya daga cikin manyan batutuwan da masu amfani da Twitter a Iran suka fi yin tsokaci a kansa.

Akasarin matan da suka yi tsokaci a kai sun bayyana cewa an rika taba jiki ko rungumarsu a cikin Harami.

An yi ittifaki cewa sama da mutum miliyan biyu ne ke yin aikin Hajji a duk shekara, inda ake yin taruwar da babu wani addini da ke hada dandazon mutane irin wannan.

A Najeriya ma wasu mata da dama sun shaidawa BBC cewa irin haka ta faru da su a lokutan aikin hajji ko Umra, amma ba su bayyana hakan a shafukan sada zumunta kamar yadda 'yan wasu kasashen suka yi ba.

Matan sun ce amma saboda tsari na al'adar Bahaushe sai suka yi gum da bakinsu ba su shaida wa kowa ba. Sai dai wasu sun ce tun a haramin suka gayawa 'yan sanda da ke gadin wajen wato Askar.

"Ni kam a take na nuna wa wani Askar mutumin kuma sun dauki mataki a kansa," in ji wata da ta bukaci a boye sunanta.

Musulunci dai ya umarci mata su rika rufe jikinsu daga kai zuwa kafa domin su kare martabarsu da kuma kokarin kare yaduwar fasadi tsakanin maza da mata.

Wasu matan kuma sun ce baya ga cin zarafi yayin ibada ma an yi ta kokarin neman yin lalata da su a motoci ko yayin da suka je sayayya shaguna a lokacin aikin hajji.

Mata da dama a kasashe irinsu Iran da Saudiyya da Masar, da kuma Afghanistan sun ce har yanzu suna fuskantar cin zarafi a kan hanya, duk da sanya kaya masu rufe jiki da suke yi, wanda hakan ke nuna cewa mutane ba sa martaba dokokin musulunci yadda ya kamata.

Masu amfani da maudu'in #MosqueMeToo sun ce ana cin zarafinsu ko da a wuraren ibada masu sauki ne, kuma ko da jikinsu a rufe yake kuma suna Sallah.

Masu amfani da Twitter a Iran sun bayyana yadda aka ci zarafinsu a wuraren aikin Hajji, kuma sun kalubalanci masu cewa sanya hijabi yana hanawa a ci zarafin mata.

Labarai masu alaka