'Duk wata ina ba da cin hanci don kar a rusa kabarin kanwata'

Hakkin mallakar hoto Amirul Rajiv
Image caption Suraya Parveen ta ce kabarin shi ne abu na karshe da zai iya tuna ma ta da mahaifin ta Mejbah Uddin Ahmed

Yawancin kaburbura a birnin Dhaka mai cunkoson jama'a na wucin gadi ne, saboda gwamnatin Bangladesh na fuskantar karancin makabartu.

Amma me za ka iya yi idan wani mamaci ya gaje makwancin wani naka da ya mutu?

Suraya Parveen ta daina kai ziyara makabartar da aka binne mahaifinta don yi masa addu'a, saboda an binne wani mutum da ba ta san ko waye ba a inda aka binne nata mahaifin.

Suraya ta shaidawa BBC a wata hira da ta yi a dan karamin gidanta da ke birnin Dhaka cewa: "A matsayina na babba a gidanmu, alhakin kula da komai ya rataya a wuyana.

Wata rana sai na tambayi dan uwana ko ya kai ziyara kabarin mahaifinmu a dan tsakanin?''

Bayan ya dan jinkirta, sai ya shaida mata an samu wasu karin sabbin kaburbura a kan kabarin mahaifinsu.

"Wasu mutanen na daban ne suka gaji kabarin, saboda anan aka binne dan uwansu kuma tuni suka yi wa kabarin siminti.

Wannan abu ya tsuma ni, don na dauki dogon lokaci ban san abinda zan fada ba,'' ta fada cikin share hawaye.

Makabartar Azimpur a Dhaka Hakkin mallakar hoto Amirul Rajiv
Image caption Kaburbura a wata makabarta

"Da na san haka za ta faru, da na yi wani kokarin kubutar da kabarin. Saboda kabarin shi ne abu na karshe da yake tuna min da mahaifina.''

Za ta iya ci gaba da kai ziyara karamar makabartar mai suna Kalshi, amma kabarin mahaifinta ya zama tarihi don ko alamunsa ba za ta gani ba. An binne wani mamacin na daban.

Ba wannan ne karon farko da Suraya ke samun kanta cikin hali irin haka ba.

Ta rasa kabarin babban danta, da mahaifiyarta da kuma kawunta kamar dai yadda ya faru da na mahaifinta.

Wannan matsala dai ta bar mutane da dama a birnin cikin halin bakin ciki saboda ba su san inda za su kai ziyara ba, idan za su yi wa 'yan uwa da masoyan da suka rasu addu'a.

Ba abu ne mai wahala ba samun wurin da za a binne mamaci, saboda kaburburan wucin gadi sun fi komai arha a makabartun kasar.

To amma karkashin dokar birnin, duk bayan shekara biyu da binne mamaci za a iya binne wani a kabarin.

Don haka ake ganin a rami daya akan binne mamata babu adadi a cikin 'yan shekaru.

Wata mace tsaye gaban wani kabari a makabartar Azimpur Hakkin mallakar hoto Amirul Rajiv

Babu wani abu da mutane za su yi, don haka ake ci gaba da binne mamata a tsaffin kaburbura.

Kone gawa, ko zuba sinadarin danya ta zagwanye ba abu ba ne da kai tsaye addinin musulunci ya amince da shi. Don haka musulman kasar ba su amince da yin haka ba.

Yawancin iyalai kan kokarta rike wurin da aka binne wani dan uwansu don su ci gaba da binne mamatansu.

Tun a shekarar 2008 hukumomin birnin Dhaka suka dai na ba da kabari na dindindin, kuma idan za ka sayi kabarin da za a iya kira na dindindin da zai dauki dogon lokaci ba tare da binne wani a wurin ba.

Kabari da ke daukar lokaci ba a binne wani a wurin ba kan kama daga Dala 20,000 a kasar da yawancin mutane ke daukar dala 1,610 a shekara.

Makabartar Azimpur da ke kusa da wata tsohuwar makabarta da a baya ita ce mafi girma a Bangladesh, da kuma aka binne dubban mamata a yanzu ita ma an fara mata garanbawul din bin tsarin binnewa na zamani.

Wani mai hakar kabari a makabartar Azimpur Hakkin mallakar hoto Amirul Rajiv

Makabartar ta cika makil da allunan da ke nuna alamar kabarin mamaci da suna da shekarar rasuwa, ko wanne bangare na makarabartar dai ya gama cika don haka ne dole a a sake binne wasu sabbin mamata a tsofaffin kaburbura.

Wata matashiya mai suna Sabiha da ta hallaka kanta shekara 12 da suka wuce, 'yar uwarta mai suna Begum ta tabbatar da shekara 10 kenan ta na bai wa masu gadin makabarta da masu hakar kabari na goro don su kare kabarin 'yar uwarta don kar a binne wani mamaci a wurin.

"Ina kewar 'yar uwata, kullum gani na ke wata rana za ta dawo. A wasu lokuta na kan je kabarinta in yi ta magana da fatan wata rana za ta amsa min, Na kan bata labarin sabbin fina-finan da suka fito na kuma kallah, da wakoki.Na kan ji kamar ta na raye kuma da ita muke hira, ba abu ne mai sauki ba ka bayyana yadda ka ke ji a lokacin da ka samu kan ka a halin da na ke ciki.''

A duk shekara, masu gadin makabarta kan kira ta, ta wayar tarho idan kabarin 'yar uwarta na cikin barazanar binne wani a wurin, kuma daman su ta ke bai wa na goro don kare shi.

"A lokacin da aka binne ta mun san cewa ba a ba da kabarin dindindin ba.

"Watanni 18 zuwa 22 da binne ta, kai ba ma dai zan iya tunawa ba gaskiya, masu gadin makabartar su ka kira ni tare da shaida min za a rushe kabarinta.

"A lokacin na shiga tsananin damuwa da neman hanyar da zan kubutar da kabarinta daga rushewa,'' in ji Sabiha.

Wani ya na ban ruwa a makabartar Azimpur Hakkin mallakar hoto Amirul Rajiv

"Mutumin da na ke biya don kula da kabarinta, shi ya fada min idan zan saki kudi za a iya kare kabarin daga rushewar hukuma, don haka tun daga wancan lokacin na ke ba su kudi har kawo yanzu.

"A duk shekara, tsakanin watan Agusta ko Fabrairu, mai kula da kabarin ya na kira na ta wayar tarho don shaida min lokacin rusau ya yi, don haka sai na dan ba shi wani abu baya ga kudin da na ke badawa ga wanda ke kare min kanarin Begum duk wata tamkar albashi.

"Ta wannan hanyar na ke ta kula da kabarinta tsahon shekara 12.''

Kamar yadda malaman addini a kasar Banladesh suka bayyana, addinin musulunci ya amince da binne gawar sama da mutum guda a kabari daya.

Sai dai abin da 'yan uwan mamata ke bukata shi ne a binne dan uwansu a kabarin sa shi daya ba tare da wani ba.

Sai dai a birnin Dhaka, wannan ba ta samuwa komai karfin imani da addininka.

Babbar cocin roman Katolika ta Holy Rosary, da ke makabartar da ake binne mabiya darikar Katolikar na fidda wata sassanyar iska.

Amma duk da haka, anan ma matsalar iri daya ce, kaburburan da ake gani an yi musu ado da furanni ga kuma ciyayi kwance a akasa da allon da ke dauke da sunan mamaci.

Wannan kabarin duk kyan da ya yi a ido, shi ma ya na dauke da labari mara dadi, kamar yadda limamin cocin Fada Komol Koraya ya shaidawa BBC.

''Lamarin na cike da tashin hankali, saboda yawancin mutane su na yin kaura daga wasu yankunan kasar zuwa birnin Dhaka.

Mu na kula da makabartar yadda ya kamata. Yawancin mabiya darikar katolika na son a binne su a makabartar mu saboda sun yi imanin wurin akwai rahama.''

Unplanned urbanisation in Dhaka Hakkin mallakar hoto MUNIR UZ ZAMAN
Image caption Birnin Dhaka na daga cikin birane masu cinkoson jama'a a duniya

"Sai dai matsalar ba mu da isasshen sarari, don haka a ko wacce shekara biyar sai mun rushe makabartar a kuma fara binne wasu mamatan.

"Idan ana hakar makabartar mukan ci karo da kasusuwan da ba su zama kasa ba.''

Wannan shi ne ainahin halin da makabartun birnin Dhaka ke ciki, wanda sama da mutane miliyan 16 su ke rayuwa a sararin da bai wuce Sikwaya mita 300 ba, sai an rubanya sararin sau biyar kafin a cimma girman birnin London mai al'umma kasa da miliyan tara.

Kamar yadda kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, birnin Dhaka na daga cikin birane masu cinkoson jama'a a duniya, wanda mutane sama da 44,000 ke zaune a filin da bai wuce sikwaya mita daya ba.

Haka nan birnin Dhaka ya na da makabartar gwamnati guda takwas kacal, sai kuma tsirarun makabartun da iyalai kan ware wani fili mallakinsu don binne iyalan da suka rasu.

Jami'an gwamnati da alhakin samar da karin makabartu ya rataya a kansu, na bai wa mutane kwarin gwiwar daukar mamata daga birni zuwa kauyukansu don binne su.

Haka kuma sun fara wani shirin taimakawa da motar daukar gawar zuwa kauyukansu.

Dagacin gundumar da ke kudancin birnin Dhaka, Khan Mohammad Bilal, ya ce binne mutane a kauyukansu na rage cunkoson makabartun birni.

''Watakila akwai iyalan da su ke birnin kuma su na son binne dan uwansu a kauyensu, amma ba su da halin daukar gawar saboda rashin kudin mota.

"Don haka mu anan mu na maraba da hakan kuma mu na taimakawa da abin hawa har kauyen da ake bukatar zuwa.

"Sannan mu kan dan bai wa iyalan wasu 'yan kudade don zaman makoki da kananan tsarabe-tsarabe. Wannan hanya za ta saukaka kwarai da gaske.''

Wannan matakin dai zai iya magance kashi 50 cikin 100 na matsalar da ake fuskanta a birnin, yayin da iyalai da 'yan uwa irin Suraya Parveen da Begum kan samu sassaucin kashe kudin da suke bai wa masu gadin makabarta dan kubutar da kabarin 'yan uwansu daga shafewa a doron kasa.

Da kuma zama cikin kuncin rashin nuna takamaimai wani wuri da za su kira kabarin iyaye ko na 'yan uwansu da bisa al'ada akan kai ziyara don yi wa mamaci addu'a.

Wani mutun da ya kai ziyara wani kabari a makabartar Azimpur Hakkin mallakar hoto Amirul Rajiv

Hotuna daga Amirul Rajiv

Labarai masu alaka