Birane 11 da za su iya rasa ruwan sha a duniya

Dripping tap Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kashi daya bisa uku na manyan biranen duniya na fuskantar barazanar rashin ruwan sha

Birnin Cape Town na Afirka Ta Kudu yana cikin matsanancin yanayi inda ya zama babban birni na farko a wannan zamanin da yake fuskantar barazanar rashin ruwan sha.

Haka kuma, matsalar farin da ke addabar birnin Cape Town na daya daga cikin manyan alamun da masana suka dade suna gargadi na cewa za a fuskanci rashin ruwan sha.

Duk da cewa ruwa ne ya mamaye kashi 70 cikin 100 na girman duniya, musamman ma ruwan sha, to bai fa kai yawan da mutane ke tunani ba.

Kashi uku cikin 100 na ruwan da ke kwance a duniya ne kawai tsaftatacce da za a iya sha.

Fiye da mutum biliyan daya ke fama da rashin ruwan sha, kuma mutum biliyan 2.7 ke cikin halin tsaka mai wuya na neman ruwan da za su yi amfanin yau da kullum da shi na akalla wata guda a cilkin shekara.

Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2014 kan manyan birane 500 a duniya, ya yi kiyasin cewa mutum daya cikin hudu na cikin tsananin bukatar tsaftataccen ruwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta fara ayyana wasu ayyukan samar da ruwa, Majalisar ta ce bukatar ruwa tsakanin al'umma za ta karu da kashi 40 cikin 100 a shekarar 2030, wanda yawaitar al'umma, da sauyin yanayi da yanayin rayuwar da 'yan adam ke yi za su assasa a wannan lokacin.

Bai kamata hakan ya zo da mamaki ba, idan aka kalli birnin Cape Town na Afirka ta Kudu za a tabbatar da kalubalen da ake kan hanyar fuskanta.

Ga karin manyan birane 11 da su ma ke cikin barazanar rasa ruwan sha a duniya.

1. Birnin São Paulo

Babban birnin kasuwanci na kasar Birazil, kuma daya daga cikin birane masu yawan al'umma a duniya ya taba fuskantar halin da Afirka ta Kudu ta samu kanta a shekarar 2015, a lokacin da tafkin da ake adana ruwa na kar ta kwana ya kusan kafewa da ruwan ya zama kashi hudu cikin 100.

A lokacin da aka fuskanci matsalar, birnin mai cike da al'umma sama da miliyan 21 ya kusan tsayawa cak, cikin kwanaki 20 an fuskanci matsalar da ta hada da satar ruwa da jami'an tsaro suka shiga lamarin ta hanyar sanya ido a wuraren da ruwan yake, domin kare shi daga barayi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A lokacin da matsalar ta faru, sai da ma'ajiyar birnin Sao Paulo's ta zama karkaf babu ruwa

A shekarar 2014 zuwa 2017 kudancin kasar ya fuskanci fari ma fi muni.

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi gwamnatin kasar da gaza samar da wani shirin taimakawa al'umma samun sassaucin halin da suke ciki, amma shirin da majalisar ta yi a Sao Paulo ya sake sukar lamirin gwamnatin na rashin zuba jari a wani bangare da idan bukatar ruwan ta taso za a iya samar da shi cikin sauki.

A shekarar 2016 ne rashin ruwan ya zo karshe, amma kuma a shekarar 2017 sai ma'adinar ruwan ta sake yin baya ta koma kashi 15 cikin 100 adadin da ba a yi tsammani ba a wannan lokacin kuma birnin ya sake komawa 'yar gidan jiya kan matsalar ruwan koma fiye da baya.

2. Birnin Bangalore

Hukumomin kudancin birnin a kasar Indiya na cikin matsin lamba sakamakon sabbin gine-gine, sakamakon kara tumbatsa da ya ke kara yi sakamakon zamowar birnin cibiyar Kimiyya da fasahar zamani.

Sai dai hukumomin na fadi tashin ganin an samu ingantaccen ruwa da magance matsalar magudanan ruwa.

Wani abu da ya kara janyo aka shiga mawuyacin hali shi ne sake toshewar magudanan ruwa da suke bukatar aikin gaggawa domn cire abubuwan da suka shiga manyan bututan da datti da dagwalon bandakunan mutanen yankin ke shiga ciki.

Daga bisani kuma gwamnati ta gano birnin ya rasa kusan kashi 50 cikin 100 na tsaftataccen ruwan sha.

Kamar kasar Sin, ita ma Indiya na fama da cukowar al'unmar dalilin da ke haddasa karancin ruwa, kuma birnin Bangalore ba shi da banbanci mai yawa da China in dai aka yi batun bukatun al'umma.

Sannan bincike ya gano bangaren noman rani da masana'antu na bukatar ruwa kashi 85 domin tafiyar da su amma kuma babu isasshen na amfanin yau da kullum balle kuma a wadata noman ranin.

Yayin da yawancin kududdufai da kananan koguna ba su da tsaftataccen ruwan da mutane za su sha ba tare da sun kamu da wata cuta ba misali amai da gudawa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Datti da kazantar da ta cika tafkin birnin Bangalore ba za su bari a yi amfani da shi ba

3. Birnin Beijing

Bankin Duniya ya fassara abin da ake nufi da karancin ruwa, da kwatanta hakan da idan mutane suka rasa ruwa kasa da mita 1000 na tsaftataccen ruwa ga ko wanne mutum guda a shekara.

A shekarar 2014, cikin fiye da mutane miliyan 20 ne suke cikin gararin rashin ruwa, yayin da duk mutum guda da ya kwana ya tashi a birnin Beijing yana samun ruwa mita 145 ne kacal.

Kasar China ita ce ta kwashe kusan kashi 20 cikin 100 na yawan al'ummar duniya, sai dai kash kashi 7 cikin 100 ne kadai ke samun tsaftataccen ruwan sha.

Wani bincike da jami'ar Columbia ta yi, ya yi kiyasin cewa ma'adanar ruwan China ta kafe inda abin da ya yi saura bai fi kashi 13 cikin 100 ba daga shekarar 2000 zuwa 2009.

Haka kuma cikowar da kasar ta yi da jama'a ya kara janyo matsalar.

Kididdigar da jami'an kasar suka fitar a shekarar 2015 ta nuna kashi 40 cikin 100 na ruwan birnin Beijing ya baci da dattin da ake zubowa.

Hakan ya sanya ba ma za a iya amfani da shi ba a masana'antu da ban ruwa a gonaki lokacin noman rani.

Wani kokari da gwamnatin China ta yi don shawo kan matsalar shi ne ta hanyar samar da wasu bututan da za su karkatar da ruwan zuwa wasu sassan kasar.

Sannan kuma sun samar da wani shiri na ilimantar da mutane da sanyawa 'yan kasuwa da ke amfani da ruwa karin haraji don su dauki lamarin da muhimmanci.

4. Birnin Alkhahira

Duk da kasancewar kasar Masar ita ke iko da wani kaso mafi tsoka na kogin Nilu, a halin da ake ciki zamani ya sanya kasar shiga halin ni 'yasu.

Duk da kasancewarta na diban kashi 97 cikin 100 na ruwan da Masar ta dogara da shi, a yanzu ya na cikin yanayi na kazanta saboda dattin da iyalan da ke kusa da gabarsa suke fitarwa, haka nan ruwan da ake amfani da shi don noman rani mai cike da sinadarai da taki sun kara bata shi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kashi 97 na ruwan da Misirawa ke amfani da shi ya dogara ne da Bahar Nilu

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce kasar Masar na daga cikin kasashe masu karamin karfi, da yawancin al'ummarsu ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutuka masu nasaba da ruwa mara tsafta.

Majalisar Dinkin Duniya ita ma ta ce kasar za ta shiga mawuyacin hali sakamakon rashin ruwa a shekarar 2025.

5. Birnin Jakarta

Kamar sauran kasashen duniya da ke gabar teku, shi ma babban birnin kasar Indonesiya na fuskantar barazanar tumbatsar teku.

Sai dai birnin Jakarta na cikin tsaka mai wuya sakamakon matsalar tumbatsar teku.

Saboda kusan fiye da rabin al'ummar birnin miliyan 10 ba sa samun ruwan famfo, yayin da haka rijiya ba bisa ka'ida ba ya zama babban laifi.

Wannan dalili ke haddasawa mazauna yankin matsalolin rashin ruwa da ma samun mai tsafta.

Bankin duniya ya ce babbar matsalar ita ce kusan kashi 40 na mutanen birnin su na zaune ne a kusa da teku, da zarar ya tumbatsa cikin kankanin lokaci zai shafe su.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hakar rijiya ba bisa ka'ida ba na jefa birnin Jakarta cikin hadarin ambaliyar ruwa

6. Birnin Moscow

Kashi daya na ruwa mai tsafta da ake samarwar a duniya yana kasar Rasha, sai dai kasar na cikin matsalar gurbataccen hayaki da masana'antu ke fitarwa.

Wannan ce babbar matsalar da birnin Moscow ke ciki, kashi 70 cikin 100 na ruwan da al'umma suka dogara da shi su na samu ne idan aka yi ruwan sama.

Wata kididdiga da hukumomi suka bayyana, ta nuna kashi 35 cikin 60 na ruwan da ake sha ba shi da cikakkiyar tsafta.

7.Birnin Santambul

Kididdigar da gwamnatin Turkiyya ta fitar, ta nuna kasar na cikin tsaka mai wuya na rashin ruwa tun bayan samun raguwar adadin ruwan da ake samu zuwa kubik 1,700 a shekarar 2016.

Hukumomin al'umma a yankin karkara sun yi gargadin za a iya fuskantar rashin ruwa mafi muni a tarihin kasar a shekarar 2030.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Watanni 10 kenan da fari ya afkawa wannan tafkin da ke birnin Santambul

Shekarun baya, yankuna masu cunkoson jama'a kamar birnin Santambul, ya fara fuskantar raguwar ruwa a yankunan da a baya ba su cika samun matsalar ba.

A shekarar 2014 adadin ruwan da ake samu ya ragu da kashi 30 cikin 100 a farkon shekarar 2014.

8. Birnin Mexico

A birnin Mexico kuwa, ba wani sabon abu ba ne a ce an samu raguwa a ruwan da al'ummar birnin kusan miliyan 21 za su yi amfani da shi.

Cikin gidaje biyar, daya ne kadai suke iya samun ruwan famfo na wasu 'yan sa'o'i kalilan cikin mako guda, wasu kashi 20 kuma na samun na kasa da sa'a daya a ko wacce rana.

Birnin na shigo da kashi 40 cikin 100 na ruwan da ake amfani da shi daga wuri mai nisa, sannan ba su da tsarin nan na sake tsaftace ruwa don yin amfani da shi misali a gonaki.

Yayin da kashi 40 na matsalar ana fuskanta ne saboda lalacewar bututan ruwa.

9. Birnin Landan

Cikin dukkan biranen duniya, akan yi mamaki idan aka ce birnin Landan na cikin wadanda ke fuskantar karancin ruwa.

Batun gaskiya shi ne, a shekara a kan samu zubar ruwan da bai kai na wasu kasashen ba.

Sai dai kuma birnin Paris na Faransa ma ya na fuskantar rashin yawan zubar ruwa a lokacin damuna, amma ya fi birnin New York.

Ana samar da ruwan da ake amfani da kashi 80 cikin 100 a birnin Landan daga Koguna.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kashi 25 cikin 100 na ruwan birnin Landan ana al-mubazzaranci da shi

10. Birnin Tokyo

Babban birnin kasar Japan, na fuskantar shigen matsalar da wasu biranen Amurka kan fuskanta, saboda samun yawaitar ruwan sama. Ruwan na zuba ne cikin farkon watanni goma na shekara.

Ana tsananin bukatar ruwa a kasar, saboda rashin zubar sa da yawa ko adanawa ka iya janyo fuskantar fari.

Akalla ana samun gine-gine masu zaman kansu kusan 750 a birnin Tokyo da suke samar da ruwan da ake amfani da shi a wuraren kasuwancinsu.

Birnin Tokyo mai al'umma sama da miliyan 30, ya dogara ne da kashi 70 cikin 100 na ruwan amfani daga Kogi, da kankarar da ake narkawa da kuma ruwan sama.

A baya-bayan nan masu zuba jari sun zuba a fannin bututan ruwa, da suka ratsa ta ayyukan more rayuwar jama'a.

11. Birnin Miami

Birnin Florida na Amurka, na daga cikin biranen kasar biyar da ke fuskantar mamakon ruwan sama a ko wacce shekara.

Amma kuma wasu daga cikin manyan biranen da suka yi fice irin Miami na fuskantar rashin ruwan.

A farkon karni na 20, an gudanar da wasu ayyuka don samar da ruwa a birnin, inda aka fara janyo ruwa daga Tekun Atilantika da kuma babbar madatsar ruwa da ake amfani da ita wajen rarrabawa wato Biscayne Aquifer, da kuma baki dayan ruwan Miami ya ke tare nan.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yadda ruwan tekun Atilantika da birnin Miami ke dogaro da shi da tacewa don amfani ya cika ya batse

Duk da cewa a shekarar 1930 aka gano matsalar, amma har yanzu akwai wuraren da har yanzu suke yoyo, musamman saboda biranen kasar na fuskantar tumbatsar teku akai-akai cikin kankanin lokaci.

Da yadda ruwan ke haurowa sama kamar zai shafe gidajen da ke bakin gaba. Amma har yanzu akwai babbar barazanar kafewarsa nan ba da jimawa ba.

Labarai masu alaka

Karin bayani