Zakuna sun cinye mafarauci a Afirka Ta Kudu

zakuna

'Yan sanda a Afirka Ta Kudu sun ce wasu zakuna sun cinye wani mafaruci tas, sai kansa kawai suka bari.

An gano kan mutumin ne da sauran burbushin jikinsa a yashe kusa da wata bindiga irin ta mafarauta, a wani gandun namun daji da ke kusa na Kruger da ke yankin Limpopo a ranar Asabar da safe.

Jaridar Birtaniya ta Daily Mail ta ce, mazauna yankin ne suka fara ankara cewa wani abu yana faruwa saboda ihun da suka jiyo da kuma karar harbin bindiga.

Amma lokaci ya riga ya kure ta yadda ba za su iya kai masa agaji ba.

Mai magana da yawun 'yan sanda na Limpopo Moatshe Ngoepe, ya ce: "Mutumin dai kamar farauta yake yi a gandun dajin yayin da zakunan suka kai masa hari.

"Sun cinye mutumin, kusan ba abun da suka rage a jikinsa sai kansa da burbushin sassan jiki."

A yanzu dai 'yan sanda suna kokarin gano ko wane ne mutumin.

Sai dai babu tabbas kan ko wacce irin dabba yake farauta a lokacin da bun ya faru - amma ana tunanin ba mamaki ma farautar zakunan yake yi.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa, wata 12 da suka gabata an samu gawarwakin wasu zakuna da aka ba su guba aka kuma yanke kawunansu da

Wasu mutanen sun yi amanna cewa ana amfani da wasu bangarorin jikin zaki wajen hada maganin gargajiya.