South Africa: Shugaba Jacob Zuma ya sanar da yin murabus

Shugaban Afirka ta Kudu ya sauka daga mulki baya ya fuskacin matsin lamba sosai. Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya ce ya sauka daga mulkin kasar bayan ya fuskanci matsin lamba daga jam'iyyarsa ta ANC.

Mista Zuma, wanda ya hau mulkin kasar tun a shekarar 2009, ya yi ta fuskantar zarge-zargen cin hanci.

Amma tun a watan Disamba ake matsa masa lamba cewa ya yi murabus, a lokacin da Cyril Ramaphosa ya maye gurbinsa a matsayin shugaban jam'iyyar ANC.

Sabon shugaban jam'iyyar, Cyril Ramaphosa na kan gaba wajen neman a kawar da shugaba Zuma daga mukaminsa, domin ya maye gurbinsa.

Murabus din na sa na zuwa ne bayan wani dogon jawabi da ya yi, inda ya bayyana cewa bai amince da hanyar da jam'iyyar ANC ta bi ba a kan al'amarin.

Ya kuma ce ba ya tsoron kuri'ar yanke kauna, inda ya kara da cewa "Na yi wa jama'ar Afirka ta Kudu hidima da dukkan karfina."

Jam'iyyar ANC ta fitar da wata sanarwa inda ta ce Murabus din Mr Zuma ya bai wa jama'ar Afirka ta Kudu tabbas.

Mista Zuma dai ya kasance tsohon dan jam'iyyar ANC, bangaren rundunar soji a zamanin wariyar launin fata, har ya kai matsayin shugaban kasa.

Labarai masu alaka