Gwamnatin Kano 'ta jefa mu a kuncin rayuwa'

Kungiyar kwadago na shirin kai ruwa rana da gwamnatin Kano Hakkin mallakar hoto CHOJ
Image caption Kungiyar kwadago na shirin kai ruwa rana da gwamnatin Kano

Kungiyar kwadagon Kano da ke arewacin Najeriya ta ce za ta kai ruwa rana da gwamnatin jihar sakamakon rashin biya, da kuma tsakuren da ake yi a cikin albashin wasu ma`aikata da `yan fansho.

Kungiyar da wasu ma'aikatan sun shaida wa BBC cewa jumullar kudin da ake cirewa daga albashinsu ta kai kusan naira biliyan daya.

'Yan kwadagon sun yi kukan cewa gwamnatocin kananan hukumomi na cirar albashin ma'aikata da sunan kudin ajiya don biyan fansho, alhali a nasu bangaren ba sa ba da nasu kason, kuma wannan ne yasa 'yan fansho da dama ba a biyansu hakkinsu a kananan hukumomi.

Sai shirin inshorar lafiya, wanda 'yan kwadagon suka bukaci a dakatar da shi, saboda basu fahimci tsarin ba.

Wasu ma'aikatan da lamarin ya shafa sun ce rayuwarsu ta tagayyara.

"Na shiga kuncin rayuwa ba kadan ba, sakamakon yanke min albashi da ake yi. Ina da mata biyu da yara 12 da kuma kanne biyar a karkashina, amma sai da ta kai kanena ne ke aiko min abinci," in ji wani ma'aikaci.

Ita ma wata ma'aikaciya ta ce "Wani watan a cire maka N2000, wani kuma watan a cire N50,000 saboda mutum ba shi da takamaiman ya san nawa ne albashinsa."

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta fara daukar mataki.

Shugaban ma'aikatan jihar Alhaji Awwal Na`iya ya shaida wa BBC cewa "sai da mai girma gwamna ya kafa kwamiti ya ce lallai ne mu je mu duba wannan lamari, sannan mu tabbatar mun warware wannan matsala cikin kankanen lokaci."

Hakkin mallakar hoto KANO GOVERNMENT

Labarai masu alaka