Chelsea 3-0 West Bromwich Albion

Eden Hazzard na Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Eden Hazzard ya saka kwallo bakwai kenan a ragar West Bromwich Albion a gasar Firimiya ta bana

Eden Hazard ya jefa kwallo biyu a ragar West Brom, matakin da ya sa kocin Chelsea Antonio Conte zai sarara bayan da kungiyar ta lallasa fara dawo wa ganiyarta.

An dai fara rade-radin cewa Conte na dab da barin kungiyar bayan da ta sha kashi a hannun kungiyoyin kamar Bournemouth and Watford - amma wannan nasarar da ta kai su ga mataki na hudu a gasar Firimiyar Ingila za kwantar da hankulan magoya bayan kungiyar.

An rika rera wakoki da sunan kocin a farkon wasan, amma ko shakka babu kocin ya ji dadin kwarewar da Hazard ya nuna domin tabbatar wa mutane har yanzu yana nan kan ganiyarsa.

Hazard da Olivier Giroud sun yi wa juna fasin-fasin kafin suka ci kwallon Chelsea ta farko, inda kuma Victor Moses ya jefa kwallo ta biyu bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 71.

Hakkin mallakar hoto Rex Features

Wannan nasarar ta kai Chelsea mataki na hudu kenan, inda ta ke da maki guda a gaban Tottenham mai mataki na biyar a teburin gasar Firimiyar Ingila.