South Africa: ANC ta ba Zuma kwana 2 ya yi murabus

Jacob Zuma

Asalin hoton, Getty Images

An bai wa shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma kwana biyu ya yi murabus daga mukaminsa, inji tashar talabijin ta gwamnatin kasar, wato SABC.

Wakilin BBC Andrew Harding ya ce wannan matakin ya biyo bayan wata doguwar tattaunawa da jam'iyyar ANC mai mulkin kasar ta yi a duk tsawon ranar Litinin.

Bayan an shafe awa da awoyi ana ganawa, jam'iyyar ta ANC ta tura manyan shugabanninta zuwa wajen shugaba Jacob Zuma a fadarsa da ke Pretoria.

Rahotanni su tabbatar da cewa jam'iyyar ta ba Mista Zuma awa 48 ya mika mulki da kashin kansa, ko kuma ta yi masa kiranye.

Kawo yanzu babu wani martani daga bangaren Mista Zuma, kuma ba a san matakin da zai dauka ba.

Amma duk da haka wannan matakin ba zai yi wa shugaban dadi ba.

A daya bangaren kuma mutanen kasar ba za su gamsu da wannan matakin ba, domin jam'iyyar ANC ta yi wa al'ummar kasar alkawarin kammala komai zuwa ranar Litinin.

Kara ma shugaba Zuma kwanaki biyu da jam'iyyar ta yi ya nuna irin tsantsenin da jam'iyyar ta ANC ke yi na kaucewa kazamin rikicin siyasa, musamman a majalisar kasar.

Mista Zuma na fuskantar tuhume-tuhume dangane da zargin cin hanci da rashawa.

Sabon shugaban jam'iyyar, Cyril Ramaphosa na kan gaba wajen neman a kawar da shugaba Zuma daga mukaminsa, domin ya maye gurbinsa.

Mista Ramaphosa babban attajiri ne, kuma tsohon dan kwadago ne, ya yi alkawarin magance matsalar cin hanci da rashawa a bangaren gwamnati da kuma farfado da jam'iyyar ANC kafin zabubbukan da za a yi a shekara mai zuwa.

Amma da alama jam'iyyar na dab da darewa gida biyu, kuma shugaba Zuma ya kafe cewa kamata yayi a bar shi ya cigaba da mulkin kasar a makonni ko ma watanni masu zuwa.