An yankewa 'yan BH 20 hukuncin zaman gidan yari

Mambobin Boko Haram Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wata kotu a Najeriya ta kama 'yan Boko Haram 20 da laifin ta'addanci da kisan kai da kuma satar mutane.

Daga cikin su akwai wani nakasasshe wanda aka kama da laifin satar 'yan matan sakadanren Chibok 200 da ke arewa maso gabashin kasar a shekarar 2014.

An yanke masa hukuncin shekaru 15 a gidan kurkuku.

Wannan ne karon farko da aka yankewa wani 'dan Boko Haram hukunci bayan an same su da hannu a satar 'yan matan Chibok, al'amarin da ya tayar da hankalin duniya.

Kotun ke yi wa 'yan kungiyar Boko Haram shari'a a garin Ka'inji da Ke jihar Niger, ta kuma sallami 'yan Boko Haram guda biyu saboda rashin gamsasshiyar shaida.

Majiyoyi a kotun sun shaida wa BBC cewa za a yi wa mutun 700 da ake zargi da zama 'yan Boko Haram shari'a a wannan makon a kotunan farar hula hudu.

Hukumomin Najeriya sun ce an kama mutane fiye da dubu shida da ake zargin 'yan Boko Haram ne.

Kuma an yanke wa mutum 45 hukuncin zaman gidan yari a watan Oktoba na tsawon tsakanin shekaru uku zuwa 31 saboda an gano su 'yan Boko Haram ne.

Labarai masu alaka