An rufe gidan rediyon da ya ce mata shaidanu ne

Dakin daukan shirye shirye na gidan rediyo Hakkin mallakar hoto Getty Images

Hukumar da ke sa ido a kan kafafen watsa labarai a Rwanda ta ce ta umarci dakatar wani gidan rediyon Amurka da ke aiki a kasar bayan da ya watsa mummunan labari a kan mata.

An dakatar da gidan rediyon daga watsa labarai na wata uku.

Kwamishinan hukumar, Edmund Kagire ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kalaman sun wulakanta mata bayan sun bayyana su da munanan siffofi.

Gidan Rediyon, Amazing Grace FM, ya watsa wata huduba da Fasto Nicolas Niyibikora ya yi a ranar 29 ga watan Janairu inda ya kira mata abin tsoro, matalauta, mugaye, shaidanu da kuma wadanda ba sa jin tsoron Allah.

Ƙungiyar mata ta kasar da kungiyar 'yan jarida ta mata ta hukumar kula da kafofin watsa labaran Rwanda, sun yi tur da watsa shirye-shirye.

Gidan rediyon mallakin Gregg Schoof, mutumin da ke watsa bushara, kuma ya ce bai ji dadin mugayen kalaman da aka fada a kan matan ba.

Labarai masu alaka