Nigeria: An raba 'yan biyun da aka haifa a hade a Bauchi

Tagwayen da aka raba Hakkin mallakar hoto WhatsApp

Wata tawagar likitoci a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya, ta samu nasarar raba wasu 'yan biyu da aka haife su a hade.

Sai dai daya daga cikin 'yan biyun ce ta rayu, yayin da namijin ya rasu.

Kwararrun likitoci guda bakwai, da wasu ma'aikatan kiwon lafiya ne suka aiwatar da tiyatar raba 'yan biyun cikin sa'a biyu.

Jami'ai a jihar sun ce jaririyar da ta tsira tana samun sauki da kuma farfadwowa.

A watan Disambar shekarar da ta gabata ne aka haifi 'yan biyun. ]

Mahaifiyar 'yan biyun dai matashiya ce 'yar shekarta 20.

Rahotanni sun ce aa lokacin da aka haifi yaran daya daga cikin su ba ya numfashi, al'amarin da ya sa aka bukaci yi musu tiyatar gaggawa don raba su.

Kakakin majalisar wakilai na Najeriya, Yakubu Dogara ne ya tallafa wurin biyan kudin tiyatar da aka yi musu.

Labarai masu alaka