South Africa: Zuma ya amince zai yi murabus nan da wata shida

Jacob Zuma ya kasance shugaban kasa tun daga shekarar 2009 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jacob Zuma ya kasance shugaban kasa tun daga shekarar 2009

Jam'iyya mai mulki a Afirka Ta Kudu ANC, ta roki Shugaba Jacob Zuma a hukumance da ya yi murabus, "don ci gaban kasar".

Duk da hukuncin da manyan jagororin jam'iyyar suka yanje na yi masa kiranyen gaggawa, Mista Zuma bai sauka daga mulki ba har a ranar Talata.

Wani jami'i ya ce ana sa ran zai mayar da martani kan wannan bukata a ranar Laraba.

Jami'in ya kara da cewa, tuni Mista Zuma ya shaida musu zai yi murabus nan da wata uku zuwa shida.

Mista Zuma, wanda ya hau mulkin kasar tun 2009, ya yi ta fuskantar zarge-zargen cin hanci.

Amma tun a watan Disamba ake matsa masa lamba cewa ya yi murabus, a lokacin da Cyril Ramaphosa ya maye gurbinsa a matsayin shugaban jam'iyyar ANC.

Mista Zuma na fuskantar tuhume-tuhume dangane da zargin cin hanci da rashawa.

Sabon shugaban jam'iyyar, Cyril Ramaphosa na kan gaba wajen neman a kawar da shugaba Zuma daga mukaminsa, domin ya maye gurbinsa.

Mista Ramaphosa babban attajiri ne, kuma tsohon dan kwadago ne, ya yi alkawarin magance matsalar cin hanci da rashawa a bangaren gwamnati da kuma farfado da jam'iyyar ANC kafin zabubbukan da za a yi a shekara mai zuwa.

Amma da alama jam'iyyar na dab da darewa gida biyu, kuma shugaba Zuma ya kafe cewa kamata yayi a bar shi ya ci gaba da mulkin kasar a makonni ko ma watanni masu zuwa.

Labarai masu alaka