Gwamnatin Tanzania ta 'kona' 'yan tsaki 5,000 da ransu

'Yan tsaki

Wata jaridar kasar Kenya ta ce gwanatin Tanzaniya ta kona 'yan tsaki 5,000 da ta ce an shigar da su kasar ba bisa ka'ida ba.

An shigo da 'yan tsakin ne masu kwana daya a duniya, ta kan iyakar Namanaga da ke arewacin kasar.

Wata jami'a daga ma'aikatar kula da dabbobi, Maria Mashingo, ta shaida wa jaridar Daily Nation cewa an shigar da 'yan tsakin cikin kasar ne ba tare da bin ka'idojin da suka kamata ba.

Ta kara da cewa shigar da su kasar na iya jawo barazanar yaduwar murar tsuntsaye.

A watan Nuwambar 2017 ma, kasar Tanzaniya ta kona 'yan tsaki 6,400 a wannan kan iyakar, al'amarin da ya harzuka masu fafutukar kare hakkin dabbobi.