Daliban Bauchi 21 sun mutu a hatsarin mota a Kano

hatsari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana yawan samun afkuwar hadurra a titunan Najeriya

A kalla mutum 24 ne suka mutu da suka hada da dalibai 21 da malamansu 3 da kuma direban motar, a kan hanyarsu ta zuwa Kano daga garin Misau da ke jihar Bauchi a arewa maso gabashin Najeriya.

Mai magana da yawun hukumar kare afkuwar hadurra ta Najeriya FRSC, reshen jihar Kano, Kabiru Ibrahim Daura, ya tabbatarwa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce motar da ke dauke da daliban ta yi taho mu gama ne da wata babbar mota a titin da ke tsakanin garin Gaya da na Kaida.

Daliban dai sun taso ne daga makarantar sakandaren gwamnati ta GDD da ke garin Misau na jihar Bauchi, don zuwa ziyarar karo ilimi a birnin Kano.

Kabiru Daura ya ce 13 daga cikin mamatan maza ne yayin da 10 kuma mata ne.

Baya ga wadanda suka mutu, akwai wasu mutum uku kuma da suka jikkata, wadanda tuni aka garzaya da su asibiti.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Talata da safe, kuma tuni aka yi jana'izar mamatan kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Kazalika, hukumar FRSC ta kuma ce ko a ranar Litinin ma an yi wani mummunan hatsarin a kauyen Lambu da ke kan titin Gwarzo a jihar Kano, inda mutum bakwai suka mutu.

Mutanen dai suna cikin motar tasi ce wacce ta yi taho mu gama da wata motar.

Najeriya dai na daga cikin kasashen da aka fi samun munanan hadurra da ke janyo asarar daruruwan rayuka duk shekara.

Me ya sa jiragen sojin Nigeria ke yawan hatsari?

Daliban Kano sun yi hatsari a Lagos

Labarai masu alaka