Shekau ya koma sa kayan mata – Sojoji

Abubakar Shekau ya ce kungiyarsa ce ta kai hari Maiduguri da wasu garuruwa a jahar Borno cikin 'yan kwanakin nan
Image caption Abubakar Shekau ya ce kungiyarsa ce ta kai hari Maiduguri da wasu garuruwa a jahar Borno cikin 'yan kwanakin nan

Rundunar sojin Nigeria ta ce shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya koma sa "kayan mata da hijabi" a kokarinsa na tserewa.

Wata sanarwa daga Kakakin rundunar Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman ta ce wata majiya mai tushe ta tabbatar mata cewa Shekau yana shigar burtu ne inda ya tsere ya bar magoya bayansa.

Sanarwar ta kara da cewa ya yi hakan ne saboda ya kasa jurewa takurawar da sojoji suka yiwa mayakan.

A cewar rundunar, yanzu Abubakar Shekau yana sauya Hijabi baki ko kuma shudi don gudun kada a gane shi, kuma ganinsa da aka yi na karshe "yana sanye ne da bakin hijabi."

Rundunar ta kuma bukaci sauran mayakan Boko Haram su mika wuya ko kuma su yabawa aya zaki.

Sai dai kawo yanzu ba'a tabbatar da ikirarin rundunar sojojin ba na cewa shugaban kungiyar Boko Haram yana shigar burtu.

A baya dai rundunar sojin ta sha bayyana cewa ta hallaka shi, sai dai daga bisani ya rika fitowa a faifen bidiyo inda ya musanta hakan.

Akalla mutum 30,000 ne suka mutu a shekara bakwan da aka shafe anan rikicin na Boko Haram, yayin da wasu fiye da miliyan biyu suka rasa matsugunansu.

Labarai masu alaka