Gabon: An saki jaririya bayan biyan kudin asibiti

Five-month old Angel has been reunited with her mother
Image caption Jaririya Angel ta shafe watanni biyar na farkon rayuwarta a wani asibiti mai zaman kansa

Wata uwa ta bayyana farin cikinta bayan da wani asibiti mai zaman kansa a kasar Gabon ya mika ma ta jaririyarta wadda jami'an asibitin suka rike na tsawon watanni saboda ta kasa biyan kudin magani.

Mahaifiyar jaririya Angel ta shaida wa BBC cewa ruwan nononta ya kafe saboda an raba ta da jaririyarta na tsawon wata biyar.

Asibitin sun bukaci a biya su kudin CFA miliyan biyu (daidai da dalar Amurka 3,630), kuma an biya kudin bayan da aka nemi taimakon jama'a.

Shugaban Gabon Ali Bongo ma na cikin wadanda suka taimaka wa matar.

A ranar Litinin an kama mai asibitin akan tuhumar garkuwa da jaririyar, amma an sallame shi bayan kwana daya, inji wakilin BBC Charles Stephan Mavoungou daga Libreville, babban birnin Gabon.

Daga karshe dai an kyale jaririya Angel ta koma hannun mahaifiyarta.

Image caption An mika jaririya Angel ga iyalanta

Mahaifiyar Angel, Sonia Okome, ta fada wa BBC yadda ta ji bayan da aka mika mata 'yarta: "Na yi murna sosai da aka dawo min da ita. Amma nayi nadamar cewa ba zan iya ba ta nono ba saboda ruwan nono ya kafe bayan wata biyar da raba ni da ita da aka yi".

Ta kuma koka da yadda asibitin suka ki ba jaririyarta maganin rigakafi ko da daya.

Kudin asibitin ya taru ne saboda kwanaki 35 da aka dauka ana kula da jaririya Angel a kwalba bayan da aka haifeta tana bakwaini.

Labarai masu alaka