An daure tsohon koci a Britain

Image caption Barry Bennel ya yi koci a Crewe Alexandra kuma ya nemo wa Manchester City 'yan wasa

An daure wani tsohon kocin wasan kwallon kafa a Birtaniya bisa laifin cin zarafin yara maza tun daga shekarar 1979.

Barry Bennell, wanda a yanzu a ka fi sani da Richard Jones ya musanta laifukan guda arba'in da takwas da a ke tuhumarsa da su wadanda su ka shafi yara goma sha daya, kuma daya daga cikinsu ya ce Bennell ya ci zarafinsa sama da sau dari a lokuta daban daban.

Sai dai kuliya ya wanke shi a kan kararraki uku da aka shigar. Wasu shaidu da Bennell ya yi wa horo sun ce a lokacin da yake horonsu ya yi amfani da ikonsa a kan su, yayin da su ke da burin zama shahararrun 'yan kwallon kafa.

Barry Bennel ya yi koci a Crewe Alexandra kuma ya nemo wa Manchester City 'yan wasa.

Labarai masu alaka